Kungiyar IS ta dauki alhakin kai hari a Najeriya

Kungiyar ta dau alhakin tsare sojojin Najeriya uku Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar ta dau alhakin tsare sojojin Najeriya uku

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai mummunan hari kan rundunar Sojin Najeriya a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da ta fitar ran Laraba 2 ga watan Janairu, kungiyar ta ce mayakanta sun kashe sojoji 10 tare da raunata wasu a wani hari da ta kai barikin sojoji a kauyen Sabon Gari da ke jihar Yobe ran 31 ga Disamba.

Haka kuma, kungiyar ta ce yanz haka tana rike da sojoji uku, ta karbe motoci 3 da makamai.

A cikin sanarwar, IS ta ce mayakanta sun kai hari wani barikin soji a garin Buni Gari a jihar Yobe da kanana da kuma matsakaitan makamai, inda suka kashe sojoji hudu sannan suka karbe makamai.

Kungiyar IS dai ta zafafa ayyukanta a najeriya a watannin da suka gabata, inda ta dauki alhakin kai hare-hare da dama kan jami'an tsaron kasar musamman ma a jihar Barno.


A makon da ya gabata ne dai wasu da ake zargin 'yan kungiyar IS ne suka shiga garin Baga dake jihar Barno a arewa maso gabashin Najeriya.

Wani mazaunin garin da ya shaida lamarin ya bayyanawa BBC cewa mutanen sun kafa tutarsu a masallacin juma'a da ke garin, bayan sun shafe daren Laraba suna fafatwa da sojoji.

Daga baya ne rundunar sojin Najeriyar ta sanar da cewa za ta fitar da mutane daga garin na Baga zuwa wasu wurare masu tsaro saboda ayyukan soji da ke faruwa a yankin.

Labarai masu alaka