Jagoran adawa ya yi nasarar wucin gadi a zaben DRC

Felix Tshisekedi opposition challenger in DR Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Idan ta tabbata, Mista Tshisekedi zai kasance dan adawa na farko da ya taba cin zabe tun bayan samun 'yancin kan Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo

An bayyana jagoran 'yan adawa, Felix Tshisekedi a matsayin dan takaran da ya yi nasara ta wucin gadi a zaben shugaban kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo na watan jiya.

Hukumar zaben kasar ta ce Tshisekedi ya samu kusan kashi 39 na dukkan kuri'un da aka kada, inda ya yi fintinkau ga mutumin da ke kan gaba a kuri'un jin ra'ayin jama'a, Martin Fayulu.

Wakiliyar BBC ta ce "Hukumar zabe ta shelanta dan takarar adawa, Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya yi nasara --da kuri'u sama da miliyan 7 ko kuma kashi 38 da rabi cikin 100."

Dan takarar jam'iyya mai mulki Emmanuel Ramazin Shadari, shi ne ya zo na uku.

Mista Tshisekedi ya fada wa taron magoya bayansa da ke cike da sowa cewa zai kasance shugaba ga dukkanin 'yan Kongo.

Ya jinjina wa shugaba mai barin gado, Joseph Kabila wanda ya ce yana daukarsa a matsayin wani muhimmin abokin siyasa.

Cocin Roman Katolika ta ce alkaluman da hukumar zaben ta fitar sun saba da wadanda masu sa ido kan zaben suka tattara. Inda suka ce Mista Fayulu ne ya samu rinjayen kuri'u.

Rade-radi ya karade kasar cewa dogon jinkirin da aka samu kafin fitar da sakamakon, ya ba da dama ga shugaba Joseph Kabila mai barin gado ya cimma wata yarjejeniya da Mista Tshisekedi. 'Yan takarar dai suna iya kalubalantar sakamakon.

(Sai dai ayarin Mista Tshisekedi sun musanta rahotannin cewa ya hada baki da shugaba mai barin gado, Joseph Kabila.

Martin Fayulu ya yi watsi da sakamakon zaben, inda ya bayyana a matsayin wani juyin mulkin zabe.

Ya bukaci sanin daga inda kuri'un Mista Tshisekedi ya fito kuma ya nemi masu sanya ido kan zaben da Cocin Roman Katolika su wallafa sahihin sakamako.

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce alkaluman hukumar zaben ba su yi daidai da sakamakon da aka gani a kasa ba.