Mutum 30,000 aka raba da muhallansu a Barno- MDD

Kungiyar Boko Haram ta kai hare-hare a wasu yankunan jihar Barno a watan Janairun 2019 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kai hare-hare a wasu yankunan jihar Barno a watan Janairun 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta ce karuwar rikicin Boko Haram a cikin 'yan makwannin nan ya yi sanadiyar raba mutane fiye da dubu talatin da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta tsaurara kai hare-hare ta sama da ta kasa a kan mayakan na Boko Haram domin maida martani ga hare-haren da masu tayar da kayar bayan suka zafafa kai wa a baya-bayan nan.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ta damu matuka game da halin da farar hula ke ciki.

A bangare guda kuma rundunar sojin Najeriya ta ce ga alama 'yan Boko Haram sun labe a wasu kauyuka a kewayen birnin Maiduguri inda suka saje da jama'ar gari, kamar yadda za ku ji a a wannan rahoto na.

Kimanin mutane 20,000 ne suka iso wani sansanin gudun hijira a cikin maiduguri da ya riga ya cunkushe bayan sun sha wahalar tafiya.

Mai kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, Mr Edward Kallon ya ce ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira kuma ya tarar da su a cikin mawuyacin hali.

Ya ce suna kwana a waje, sannan suna matukar bukatar taimakon abinci daruwa da tsaftataccen wajen kwana.

Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da ke bukatar wurin kwana a Monguno ba.