Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai ya rasu

Mustapha Agwai 1 Hakkin mallakar hoto @Dantatuu

Sarkin Lafia Alhaji Dr Isa Mustapha Agwai 1 ya rasu a yau Alhamis a wani asibiti dake Abuja Najeriya bayan yayi fama da jinya.

An haifi marigayin ne a ranar 14 fa watan Augusta 1935.

An nada shi Sarkin Lafia a ranar 28 ga watan Mayu 1974.

Za a yi jana'izar marigayin ne ranar Jumma'a, 11 ga watan Janairu 2019 a Fadar Sarkin Lafia da misalin karfe 2:00 na rana.

Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura yayi ta'aziya ga iyalan mamacin da kuma masarautar Lafia da jama'ar Nasarawa.

Labarai masu alaka