Harin Nairobi: Harin Dusit2 ya zo karshe — Shugaba Uhuru Kenyatta

Wasu daga cikin maharan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin maharan

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyetta, ya bayyana cewa an kawo karshen harin da 'yan ta'adda suka kai a Nairobi, kuma an kashe dukkanin 'yan ta'adda.

'Yan bindigar sun kai harin ne unguwar Westlands da ke a babban birnin kasar a ranar Talata, inda suka kashe mutum 14.

Jami'an tsaron kasar sun bayyana murkushe harin awanni kadan bayan faruwarsa, amma har a safiyar ranar Laraba ana jin karar fashewar wasu abubuwa.

Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin, amma ba a san mahara nawa ta tura ba.

Image caption Wurin da aka kai harin

A wani jawabin da ya yi ma kasar a talabijin, Shugaba Kenyetta ya bayyana cewa maharan sun kashe mutum 14, kuma an kubutar da mutum 700.

Sai dai hukumar bayar da agaji ta Red Cross mutanen da aka kashe sun 24.

Labarai masu alaka