Hira da Festus Keyamo kan zargin da Obsanjo ya yi wa Buhari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Festus Keyamo ya mayar wa Olusegun Obasanjo martani #BBCNigeria2019

Daya daga cikin shugabannin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari, Festus Keyamo, ya mayar da martani kan kan zargin da Obasanjo ya yi wa APC da gwamnatin Buhari.

Keyamo ya yi martanin ne a wata hira da ya yi da BBC a Abuja ranar Laraba.

Ya ce kalaman Obasanjo ba su da wani tasiri yanzu saboda ta bayyana yana goyon bayan wani bangare.

A kwanakin baya ne tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kara rubuta wata wasika, inda ya soki lamirin jam'iyyar APC da Shugaba Buhari.

Ya kuma kwatanta mulkin Buhari da na Shugaban Mulkin Soja Janar Sani Abacha.