Trump ya fasa gabatar da jawabi ga 'yan majalisa

Mista Trump ya bayyana Nancy Pelosi a matsayin mai gujewa gaskiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Trump ya bayyana Nancy Pelosi a matsayin mai gujewa gaskiya

Shugaban Amurka Donald Trump ya fasa gabatar da jawabi ga zauran majalisar kasar a mako mai zuwa, bayan da suka yi ja-in-ja da kakakin majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi.

Da ma dai wasu jiga-jigan jam'iyyar Democrats, ciki har da Misis Pelosi sun bukaci shugaban ya jinkirta gabatar da jawabin saboda dalilai na barazanar tsaro.

Sai dai Mista Trump ya dage kan cewa ala tilas sai ya gabatar da wannan jawabi a ranar 29 ga watan Janairu, tun da kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ce ta tsara hakan.

Misis Pelosi ta ce komai ya sauya a yanzu kuma ba za ta bai wa shugaba izinin yin jawabi a gabansu ba har sai an sake bude ayyukan gwamnati.

Kusan ana iya cewa lamura na sake rincabewa, adaidai wannan lokaci da ma'aikata gwamnatin Tarayya dubu 800 ke sake fuskantar rashin albashi a gobe juma'a.

Ana dai ganin jawabin da shugaban ke shirin yi kamar wani kokari ne na sake dauke wa mutane hankali daga ainihin babban batun da ake ciki a kasar.

To amma, shi ne zai kasance mataki na baya-baya nan, na nuna iko tsakanin jagororin guda biyu, a ja-in-ja da suke yi kan inda kasar za ta nufa.

Babu daya daga cikin bangarorin biyu da ke nuna wata alama ta sassautawa a kan samar da kudin aikin gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nancy Pelosi ta ce babu batun gabatar da jawabi a gaban majalisa har sai gwamnati ta dawo da ayyukanta

Sannan kuma dokokin biyu da ake ja-in-ja a kan su, na neman sake bude harkokin gwamnati, bisa ga dukkan alamu ba za su yi nasara ba, idan 'yan majalisar dattawa suka kada kuri'a a yau.

Mista Trump dai ya ce bai yi mamakin abubuwan da ke faruwa ba saboda irin martanin da ya ke samu daga Misis Pelosi, da kuma bayyana 'ya'yan Jam'iyyar Democrats a matsayin gangararu.

Labarai masu alaka