Rikicin 'yan takarar APC bai kare ba a Zamfara

Gwamna Abdulaziz Yari ya so kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris ya gaje shi
Bayanan hoto,

Gwamna Abdulaziz Yari ya so kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris ya gaje shi

Kasa da mako uku a gudanar da zabuka a Najeriya, dambarwar tsayar da 'yan takarar APC a jihar Zamfara da ke arewacin kasar na sake daukan sabon salo.

Kotuna biyu a jiha da Tarayya sun yanke hukunci a rana daya da suka ci karo da juna kan matsayin zaben fitar da 'yan takarar jam'iyyar APC a Zamfara.

Yanzu ana dakon matsayin hukumar zabe game da hukuncin da kotunan guda biyu suka yanke kan takaddamar zaben na fitar da gwani.

Hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja, ya tabbatar da matsayin hukumar zaben kasar na haramta wa duk 'yan takarar jam'iyyar APC daga Zamfara shiga zabukan kasar da za a yi cikin watan gobe da na jibi.

Hukunci ya yi karo da na wata babbar kotun jihar karkashin mai shari'ah Muhammad Bello Shinkafi, da ta tabbatar da hukuncin cewa jam'iyyar APC reshen Zamfara ta gudanar da zabukan fitar da gwani, don haka hukumar zabe ta karbi 'yan takararta don shiga zabukan kasar.

Sai dai mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta kotun tarayya ta zartar da hukunci cewa babu laifin hukumar zaben Najeriya, APC ce ta gaza yin sahihin zabe a lokacin da INEC ta kayyade, don haka kin karban sunaye 'yan takarar a zaben watan gobe da na jibi yana cikin huruminta.

Hukuncin ya zo ne kan wata kara da wasu suka shigar da sunan jam'iyyar APC suna ikirarin cewa su ne 'yan takararta bayan wani zaman maslaha da jam'iyyar ta gudanar a jihar Zamfara.

A zanatawarsu da BBC dukkanin bangarorin biyu da ke wannan dambarwa sun yi marhaba da wannan hukunci, sai dai a cewar su hakan wani karfafa masu gwiwa ne kan hukunci farko da kotun Jihar Zamfara ta yanke.

Hukumar INEC dai ta ce ba za ta ce komi ba a yanzu har sai hukuncin kotu ya zo gabanta kafin ta yanke shawarar ko jam'iyyar APC za ta iya gabatar da 'yan takarara.

Rikicin siyasa a Zamfara dai ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.

Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke shi saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.