Kwana 20: Yadda siyasar Najeriya ta tasirantu da mulkin karba-karba #BBCNigeria2019

Umaru Musa 'Yar'Adua Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marigayi tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar'Adua

Daga Chris Ewokor

Karin haske game da tushen asalin kalmar kebance sashe da wata al'ada (ko killace yanki da wata ta'ada), wato kalmar Ingilishi ta 'zoning' tare da ma'anar da aka juya mata a harkokin mulkin siyarar Najeriya, tare da tasirinta.

Kalmar "Zoning," wadda ma'anarta a Hausa ke nufin kebance wani sashe (ko yanki) da wata al'ada, tsari ne na yin dokokin killace fadin kasa da akan gindaya ka'idojin amfani da wurin, wato kamar daidaita irin gine-ginen da ake so a yi (tsarin kasuwanni ko rukunin gidajen unguwannin da mutane ke kwana), wadanda ta yiwu a gina ne bisa la'akari da yawan al'ummar yanki.

Tashin farko akan aiwatar da irin wadannan tsare-tsaren ne a sasssan birni, inda akan cimma muradin da aka nufa ta hanyar raba fadin kasar zuwa gunduma-gunduma (gundumomi), inda kowacce (gunduma) daga ciki na da ka'idojinta, wadanda suka shafi filaye da gine-ginen da doka ta yadda a yi.

Tare da bin sauran tsare-tsaren fasalta birni, kebance sashi muhimmin mataki ne da ke bayar da damar yin fasali bisa doka da oda a birane.

Bayanin ma'anar Kalmar kebance sashe (ko yanki) wato a Ingilishi 'zoning' ta fito ne daga babban kundin bayanai na Birtaniya, wato 'Encyclopaedia Britannica.'

A fannin siyasa kuwa, ma'anar na bayyana yadda ake fitar da ka'idar bunkasa birni.

A kasashen da suka ci gaba irin su Birtaniya da Amurka wannan shi ne hakikanin gaskiyar lamari. Mafi yawan ma'anar da aka fito da ita, ta nuna gazawa wajen bayyana irin ma'anar da aka juya (wa Kalmar) a kasashe masu tasowa irin Najeriya.

Tarihin siyasar Najeriya cike yake da hargitsi! Akwai tashe-tashen hankula da dabanci! Sai dai babbar matsalar da ake fama da ita ita ce rabuwar kai (a daukacin bambancin yanki da na addini) tsakanin Yankunan Arewaci da Kudancin kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

Yakin neman zabe akan dora shi ne kan doron tafarkin barakar da ke tsakanin al'umma.

A lokuta da dama, 'yan siyasa daga kowane sashe na kasar sun saba amfani da bambancin addini da kabilanci don jan ra'ayin masu kada kuri'a - sukan tunzura wani sashe na kasar ya soki lamirin wani a wajen kokarinsu na kankane harkokin mulki.

Wannan mummunar gaba da kiyayya da ake cusa wa al'umma, ta kan haifar wa mutane su ji cewa an danne su (an tauye su). Sukan jefa mummunan jin zafin wariya (da aka yi musu).

Shiga cikin tarihi kan al'amuran siyasa da suka wakana a Najeriya tun lokacin da aka samu 'yancin kai, na nuni da cewa kafin juyin mulkin soja na shekarar 1966, kasa ce dunkulalliya da masanan taswirar kasa suka bayyanata a matsayin "turakun murhu": Yankin Arewa da Yankin Kudu maso Gabas da Yankin Kudu maso Yamma. Kowane yanki na da gwamnatinsa.

Akwai gwmanatin da ke jan ragama a tsakiya, amma ta kafu ne da jami'ai da aka zabo su wakilce su a tsakiya. Kowane yanki ya bunkasa ne gwargwadon tafarki da yake tafiya a kai. Sai dai bayan da sojoji suka kwace ragamar mulki suka karkasa kasar zuwa jihohi, inda aka mayar da yanki guda ya kankane harkokin jan ragamar mulki.

An yi yakin basasa wanda a karshe sassan yankunan Najeriya suka karke da jin cewa sun kaskanta an tauye su, an danne su. Wannan manufa da aka wassafa a tunani ta yi matukar cutar da al'umma ne saboda tsawon lokacin da sojojin da suka fito daga wani yanki suka yi ta shugabancin kasa.

Najeriya ta koma kan tafarkin dimokuradiyya ranar 29 ga Mayun 1999 bayan an shafe shekaru 16 soja na jan ragamar mulki. Shigowar siyasar jam'iyya ya kasance tamkar bude sabon babi, kuma wata dama ce ga shugabannin siyasa su sake tantance tsarin da ya kamata a bi wajen raba madafun ikon jan ragamar kasa, ta yadda za a karfafa hadin kai da dunkulewar kasa.

Bisa wannan dalili ne ya sanya jam'iyyar da ta lashe zaben shugaban kasa, Jam'iyyar PDP ta cimma matsaya ta fito da tsarin hadin kai a tsakanin mutanen Najeriya da ke damfare da bambance-bambance.

Kebance wani yanki ana masa kallon tsarin siyasa na raba madafun iko: shirin da ke fifita karba-karba (a tsakanin yankunan kasa) wajen zabo dan takarar shugabancin kasa a tsakanin Kudu da Arewa ta hanyar yarjejeniyar da ba a tabbatar da ita a hukumance ba. PDP ta aiwatar da tsarin kebance karbar mulki a hannun wani yanki na kasa a tsakanin Arewaci da kudancin kasar nan.

Masu lura (da nazarin) harkokin siyasa na ganin yin hakan ya zama dole, don kauce wa yanayin da zai ta bai wa wani yanki na kasar ya yi ta samar da 'yan takarar shugabancin kasa.

Lamari mafi muhimmanci shi ne a fahimci yadda aka yi tsarin kebance mulki ga wani yanki ya shiga kundin siyasar Najeriya? Usman Mohammed, Farfesa a fannin nazarin kimiyyar siyasa, Jami'ar Jihar Kaduna, kuma Shugaban Hukumar Amintattu na kungiyar yin masalaha da wanzar da zaman lafiya, wadda ba ta gwamnati ba, da ke Nazarin Bincike kan rikici da wanzar da zaman lafiya, ya bayyana cewa tushen asalin "kebantar yanki da harkokin mulki" ya samo asali ne a Gwamnatin Ibrahim Babangida.

Ya yi nuni da cewa kirkirarren furuci ne da sojoji suka yi da zimmar tabbatar da daidaito da raba daidai da adalci, ta yadda za a yi daidai-wa-daida a wakilcin jagorancin al'umma, don a kauce wa siyasar danniyar karkata akala.

"Idan alal misali kowace jiha a Arewa maso Gabas da ta hado da Yobe da Barno da Gombe da Bauchi da Adamawa, ba ta da wakilci a wani mukami saboda da rashin mai ilimin da ya cancanta (a dora shi kan mukamin), kowace jiha za a iya ba ta dama ta cike gurbin. Don haka sai aka bullo da tsarin kebance mukami ga wani yanki, dabarar masalaha da ta za ta bai wa jihohi damar rike mukamin kula da tattalin arziki ko shugabancin siyasa da dabarun bunkasa tattalin arziki..

Daga bisani aka samar da sassan yankun siyasa shida, wadanda suka hada da: Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas. Wannan tsari ne na warware matsalolin siyasa cikin hanzari, don hakikanin gaskiya ma masalaha ce ga sassan yankunan siyasa kan al'amarin da ya jibinci mukaman gwamnati da tsarin zabe da tsare-tsaren tattalin arziki, tattare da fa'idojin da ke haifar da bunkasa.

A tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 alamu sun nuna yadda tsarin ya warware takaddamar masu ra'ayin siyasa mabambanta a fadin kasar nan. Tashin farkon kafuwar wannan dimokuradiyyar, Janar AbdulSalami Abubakar, Musulmi daga Jihar Neja yankin Arewa ta Tsakiya ya mika ragamar mulki hannun Olusegun Obasanjo, Kirista daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Bayan da ya kammala wa'adin mulki na zango biyu, sai tsarin karba-karba ya sanya Jam'iyyar PDP ta zabo dan takararta daga Arewa, Umar Musa 'Yaraduwa, shi ma Musulmi.

Amma bayan shekaru biyu yana jan ragamar mulki sai ya mutu, don haka mataimakinsa, Goodluck Jonathan ya zama shugaban kasa kwatsam bayan mutuwar shugabansa.

Hakkin mallakar hoto FLORIAN PLAUCHEUR
Image caption Tsohon shugaban Najeria Goodluck Ebele Jonathan

Mista Jonathan Kirista ne daga yankin Neja-Dalta da ke kudancin kasar nan. Ya kamala cikon 3wa'adin shekaru hudun ''Yaraduwa, sannan ya kakaba kansa a matsayin dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 2011.

Wannan matakin da ya dauka shi ya hargitsa tsarin karba-karba na jam'iyyar (a tsakanin yankunan kasar). Sakamakon hakan ya hadu da mummunar adawar kin amincewa da takararsa ta shugaban kasa a yankin Arewacin Najeriya.

Da yake jawabi ga magoya bayan jam'iyya a shekarar 2011, lokacin da yake yakin neman zaben Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasa Olusegun Onbasanjo cewa ya yi, "Mu ankarar da kanmu abin da Kundin tsarin mulkinmu ke kunshe da shi, inda ya tabbatar da manufar tarayya, kuma mu kadai ne jam'iyyar siyasa da ke tabbatar da tarayya a kundin tsarin mulkinmu ta hanyar kebance mulki ga wani yanki da tsarin karba-karba.

Kuma muna alfahari da hakan. A wajenmu da nan gaba za mu ci gaba da kare tsarin. Ni mai fafutikar goyon bayan tarayya ne a karkashin Gwmanatin Murtala/Obasanjo, yanzu kuwa bazan dawo daga baya in yada wata manufar daban ba. Dole ne a fahimci rudanin tarihin da ya auku ba da dadewa ba, lamarin da ya faru ba zato ba tsammani, kuma PDP a matsayin jam'iyya ta shawo kan matsalar."

Mista Obasanjo da kansa ya taba afkawa cikin badakalar gadon jan ragamar mulki a shekarar 1976, lokacin da aka kashe shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Murtala Muhammad a wani juyin mulki da bai samu nasara ba. Obasanjo ya zama shugaban kasa. Ya fito ne daga yankin Kudu maso Yammacin kasar nan. Bayan da ya shirya zabe a tafarkin dimokuradiyya cikin shekarar 1979, sai ya mika ragamar mulki ga Alhaji Shehu Shagari dan Arewacin Najeriya al'amarin da ya yi tasiri matuka wajen yin karba-karba a mulkin kasar nan tsakanin Arewaci da Kudancin kasar nan.

An kawar da Shagari daga mulki a juyin soja na Janar Muhammadu Buhari, wadanda daukacinsu 'yan Arewacin Najeriya ne, inda suka yi ta karbar mulki a tsakaninsu. A tsakanin juyin mulki da aka yi da dama, an gudanar da zabe a ranar 12 ga Yunin 1993, amma sai aka soke zaben kafin a sanar da wanda ya lashe zaben. An nuna alamun cewa Mashood Abiola ne ya lashe zaben, wanda ya fito daga Kudu maso Yamma. Daga bisani ya mutu a wani yanayi cike da rudani bayan da aka tsare shi a karkashin Gwamnatin soja ta Janar Sani abacha.

Lokacin da Najeriya ta sabunta dimokuradiyyarta a shekarar 1999, an zabo Olusegun Obasanjo ne daga yankin Kudu maso Yammaci, inda ya yi takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar PDP, a wani yunkuri na dadada wa yankin don rage jin radadin asarar MKO Abiola da ya yi. A bayyane yake karara an zabo shi ne da manufar tausasa fushin mutanen yankin Kudu maso Yamma; amma PDP ta cimma matsayar kebe mulki (da tsarin karba-karba a tsakanin yankuna) a matsayin jigon manufar tsarin kundin mulkinta.

A littafin da ya rubuta mai taken 'Tsawon jan ragamata,' tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya danganta adawar da ya fuskanta a takararsa ta shekarun 2011 da 2015 da tsarin karba-karba. Ya yi nuni da cewa Najeriya cukurkudaddiyar al'umma ce da ke bukatar dimbin nazarin ilimi kafin a fahimci hakikanin bambance-bambance da ke cikinta. Arewacin Najeriya (mai dimbin Musulmi) ta shafe tsawon zamani wajen fafutikar jan ragamar mulki a siyasar kasa. Wannan hamshakiyar fafutika ita ce aka cukurkuda aka daure Najeriya da ita.

"Lokacin da na yi takara a shekarar 2011 tare da Namadi Sambo a matsayin mataimakina, wasu shugabannin Arewacin Najeriya sun harzuka da wannan matsaya da na dauka ta yin takara. Sun yi ikirarin cewa wa'adin mulkinsu ne ya zagayo na shugabancin kasa. Sun tayar da jijiyar wuya wajen takaddamar kundin tsarin mulkin jam'iyyata. PDP.

Lamarin ke nan ya tashi daga kan Najeriya. Dalilin da suka bayar shi ne Gwamnatin Shugaba Obasanjo, Kirista daga Kudu ba dadadewa ta kammala wa'adinta na shekara takwas ba. 'Yan Arewa da dama (dimbin Musulmin da ke Arewacin Arewa) sun bayyana ra'ayinsu game da ci gaban jan ragamata. Bukatarsu in watsar da damar da kundin tsarin mulki ya ba ni. Kasancewa mun kama ragamar mulki ne a matsayin shugaba da mataimaki, ita ce gaskiyar da aka yi watsi da ita ta hanyar dabara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon Shugaban Najeriya Abdulsalam Abubakar tare da tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton

Wannan shi ne bude sabon babi a cukurkudaddiyar al'ummar kasarmu. Barakar shugabanci na nan kwance, inda ake fakewa da dalilai da dama (don cimma wata manufa). Abin takaicin shi ne, bisa wannan ma'aunin yaudarar ne duniya ke kallon Najeriya ta kimanta matsayinta. A lokacin zaben 2015 takaddama ta rura wutar rikici. 'Yan Arewa sun jajirce kan cewa mulki ya dade a hannun Kiristan Kudu tsawon shekaru 13, don haka a dawo musu da shi.

Kodayake a iya cewa tsarin karba-karba (a tsakanin yankuna) ya samu gindin zama a siyasar Najeriya, mutane da dama ba su gamsu da shi ba. Tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, kuma dan takarar shugabancin kasa, Donald Duke ba da dadewa ba ya sauya sheka daga Jam'iyyar PDP, saboda jam'iyyar ta kebe takarar shugaban kasarta na shekarar 2019 ga yankin Arewa. Mista Duke ya yi wa'adin mulki na zango biyu matsayin gwamna a karkashin tutar jam'iyyar PDP, amma dole ya fice daga jam'iyyar, don cimma burinsa na takarar shugaban kasa.

Ya ce tsarin kebance jan tragamar mulki (karba-karba) bai dace da kasar nan ba, saboda kafa ce kawai aka bayar ta samar da shugabannin da ba su da nagartar da za su iya jan ragamar mulkin kasar nan.

Yunkurin Duke na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2007 ya ci tura ne saboda PDP ta kebe takararta (ta shugaban kasa) ga yankin Arewa. Inda marigayi Umaru Musa 'Yar'aduwa ya lashe zaben. Kawai sai Mista Duke ya sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP ranar 4 ga Satumbar 2018, domin a cewar Duke tsarin PDP na karba-karba (kebancewa a tsakanin yankuna keta haddin manufofin da a da ta ginu a kai ne).

Ya fada wa BBC cewa, "tsarin bai amfanar da kasar nan ba. Sabanin ma a ce an zabo mutum mafi nagarta, sai kawai aka kebe wani yanki da zai fito da shugaban kasa. Ko da 'yan takarar yankin sun cancanta ko ba su cancanta ba - wannan dai ba shiri ba ne da ke tabbatar da nagarta. Babban barkwanci ne! Wannan shi ne dalilin da ya sanya kasar ta kasa ci gaba.

Kafin zaben 2019, tsarin kebance wani yanki (na karba-karba) an dauke shi da matukar muhimmanci. Manyan jam'iyyu biyu - jam'iyyar APC mai mulki da jam'iyyar adawa ta PDP sun zabo 'yan takararsu ne daga Arewacin kasar nan. Shugaba Muhammadu Buhari mai ci a halin yanzu, wanda ke neman a sake zabarsa a karkashin tutatar jam'iyyar APC ya fito ne daga Katsina daga yankin Arewa maso yammacin kasar nan. Babban mai kalunbalantarsa kuwa, Atiku Abubakar ya fito ne daga Jihar Adamawa a yankin Arewa maso Gabas.

Al'amarin ya fito da yadda mutanen da suka fito daga yankin guda na kasar nan suke takarar kalubalantar juna. A karshe dai duk wanda ya samu nasara jan ragamar mulki na nan daram a wannan yankin na kasar nan na tsawon wani wa'adin shekaru hudu.

Sannan yanayin na nuni da cewa Kudancin kasar nan na hankoron samun jan ragamar mulki nan da farkon shekara ta 2023. Ko dai lamarin na nuni da sakarci ko nagarta wani abu ne daban da ake ta takaddama a kai. Yanzu dai, daukacin al'umma sun gamsu da yarjejeniyar.

Labarai masu alaka