Nicolas Maduro: Anya shugaban Venezuela zai kai labari kuwa?

Venezuelan President Nicolas Maduro at a press conference in Caracas Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela yana jawabi a birnin Caracas

Rikicin Venezuela ya kai har Amurka da wasu kasashen Turai sun amince wa jagoran 'yan adawa Juan Guaido a matsayin wanda ta ce shi ne shugaban kasar na ainihi ba Nicolas Maduro ba.

Bayan an shafe kwanaki ana zanga-zangar kin jinin gwamnati a Venezuela, saboda matsin tattalin arzikin da ya addabi kasar, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa kan batun, taron da kasar Amurka ta nemi a yi shi.

Wannan na biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi ne da kasashe da dama suka ce ba a gudanar da shi bisa adalci ba.

Sakataren harkokin waje na Amurka Mike Pompeo ya sanar da Majalisar Dinkin Duniya cewa lokaci ya yi da ya kamata a goyi bayan wani bangare a rikicin siyasar Venezuela. Sakataren ya ambaci shugan kasar Nicolas Maduro a matsayin wanda yayinsa ya shude:

Ya ce tsohuwar gwamnatin Maduro ta dade tana cin zarafin al'ummar kasarta... A kokarin da suke yi na samun abinci da ruwa.

Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Spaniya na cikin kasashen da suka bi sahun Amurka wajen amincewa da jagoran 'yan adawa na kasar Guaido a matsayin zababben shugaban kasar na wucin gadi, idan Maduro bai nemi a shirya sabon zabe ba acikin kwana takwas.

Amma har yanzu Maduro na da sauran masu mara masa baya - musamman ma Rasha. Jakadanta a Majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia ya soki gwamnatin shugaba Trump - inda ya ce ta shirya juyin mulki ne kawai a Venezuela.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwamitin Tsaro na MDD yana zama a kan batun Venezuela

Shugaba Maduro da kansa ya ce dala miliyan 20 da Amurka ta yi alkawarin samar wa domin ayyukan taimakon jin kai ga sabuwar gwamnatin rikon kwarya "yayi arha a matsayin lada ga masu son juyin mulkin", kuma ministan harkokin waje na Venezuela ya yi watsi da bukatar ta kasashen Turai na a shirya wani sabon zabe a kasar nan da kwana takwas.

Labarai masu alaka