Amurka ta gaji da yakin Afghanistan

Dakarun Amurka a Afghanistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Amurka a Afghanistan sun kai 17,000

Amurka na wani taro da sashin siyasa na kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan da ke Qatar domin kawo karshen rikicin kasar da aka shafe shekara 17 ana tafka wa.

Jakadan da ke wakiltar Amurka a wajen taron ya ce ana samun cigaba mai ma'ana a wannan tattaunawar da ake yi.

Wasu majiyoyi a cikin kungiyar ta Taliban kuma sun tabbatar da an sami daidaito kuma an dab da rattaba hannu kan wani daftari na 'yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla.

Amurka dai na son samar da tabbataccen zaman lafiiya a kasar, da yaki ya daidaita al'u'marta.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jakadan Amurka na musamman a Afghanistan Zalmay Khalilzad

Shugaban Amurka Donald Trump na son ganin dakarun kasar da ke Afghanistan sun koma gida bayan yunkurin da yayi na janyde dakarunsa daga Syria.

Dakarun Amurka sun shafe shekara 17 a kasar, a wannan yakin da ya kasance mafi dadewa da kasar ta yi a tarihinta.

  • Bayan an shafe kwanaki shida ana tattaunawa tsakanin wakilan kungiyar Taliban da jami'an Amurka a yankin mashigar Tekun gabas ta tsakiya, rahotanni na cewa ana samun cigaba a kan wasu batutuwa biyu masu muhimmanci:
  • Na farko shi ne lokacin da dakarun Amurka za su kwace kayansu su fice daga Afgahanistan. Na biyu kuma shi ne Amurka na son ta sami tabbaci daga kungiyar Taliban cewa ba za ta bari kasar ta fada hannun kungiyoyin ta'addanci na kasa da kasa ba kamar al Qaeda.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Afghanistan a yayin da suka kamo wasu 'yan

Amma kawo yanzu ba a fitar da wata sanarwa ba a kan batun tsagaita wuta a yakin da aka shafe shekaru ana yi, kuma har yanzu kungiyar Taliban ba ta amince ta fara tattaunawa kai tsaye da gwamnatin kasar a birnin Kabul ba.

Jakadan Amurka na musamman a Afghanistan Zalmay Khalilzad zai tafi Kabul daga Qatar domin sanar da shugaban Afganistan Ashraf Ghani game da ci gaban da aka samu.

Labarai masu alaka