Firai minista Justin Trudeau ya kori jakadan kasarsa a China

Jakada McCallum tare da Justin Trudeau Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jakada McCallum tare da Firai minista Justin Trudeau

Firai minista Justin Trudeau ya kori jakadan kasarsa a China kwanaki bayan ya ce Kanada ta yi kuskuren kama wata babbar jami'ar kamfanin Huawei.

Korar jakadan ta biyo bayan wasu kalamai da Mista McCallum din ya furta game da batun nan na kama wata babbar jami'ar katafaren kamfanin Huawei mai samar da kayan sadarwa da Kanada ke rike da ita.

Firai ministan ya sanar da cewa shi ne ya nemi jakadan ya ajiye mukaminsa, amma bai bayyana dalilin daukar matakin ba.

Hukumomin kasar Kanada sun kama Meng Wanzhou ne a ranar 1 ga watan Disamba a birnin Vancouver da ke yammacin kasar bisa wani sako daga Amurka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Meng Wanzhou ta musanta dukkan tuhumar da ake ma ta

Daga baya wata kotu a birnin ta bayar da belinta akan kudi dala miliyan 7 da dubu 600, amma an saka mata wasu tsauraran matakai da suka hada da daura wata na'ura a kafarta da za ta rika bayyana wa 'yan sanda duk inda ta shiga.

A farkon wannan watan ne jami'an Amurkan suka tabbatar cewa za su nemi a mika masu Mis Wanzhou domin ta fuskanci shari'a.

A karkashin dokokin Kanada, Amurka na da kwana 60 ta mika bukatarta a rubuce na a mika mata matar, wa'adin da zai kare a karshen wannan watan.

Ma'aikatar harkokin waje ta China ta nemi jami'an Amurka su janye bukatar tasu.

Wannan batun ya kasance dalilin wata rikicin diflomasiyya tsakanin Kanada da China.

Da alama China na mayar da martani, domin a farkon wannan watan wani wata kotu a kasar ta yanke wa wani dan kasar Kanada hukuncin kisa bayan da ta yi watsi da hukuncin wata karamar kotu da tun da farko ta yanke masa hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Michael Spavor (hagu) da Michael Kovrig

Ban da shi kuma akwai wasu 'yan kasar biyu Michael Spavor da Michel Kovrig da Chinar ke tsare da su tun bayan da Kanada ta kama Mis Meng.

Wasu masu nazari siyasar China na ganin wadannan matakan na ramuwar gayya ne, amma jami'an China sun musanta haka.

Labarai masu alaka