Akwai 'yan Brazil da ke wasa a Najeriya

Rafael Everton daga kasar Brazil yana horar da kungiyar Akwa United

Asalin hoton, Twitter/@akwaunited

Bayanan hoto,

Rafael Everton, dan kasar Brazil, shi ne kocin kungiyar Akwa United

Wannan makala ce da wani mai sharhi kan harkokin wasanni a Najeriya Isiyaku Muhammad ya rubuta mana:

A yanzu haka kakar bana ta gasar Firimiyar Najeriya wadda ake kira Nigerian Professional Football League (NPFL), ta yi nisa, inda ake ta fafatawa da kece-raini tsakanin kungiyoyin wasanni.

Kakar bana ta zo da wani sauyi daban, kasancewar an tsayar da kakar bara kafin a kammala saboda wasu matsaloli.

Hakan ya sanya aka ba kungiyar Lobi Star ta Makurdi kofin kasancewar ita ce a saman taburi kafin a samu tsaikon da ya jawo gasar ta tsaya.

Sai dai wani abin sha'awa a gasar Firimiyar Najeriya shi ne, yadda 'yan wasa daga kasashen waje suke tururuwar zuwa domin bajekolinsu cikin kwanciyar hankali.

Domin kuwa duk wanda ya dauki shekara biyu zuwa uku a kasa, to lallai ya gamsu da yanayin tsari da kuma watakila yadda aka karbe shi, da kuma uwa-uba yadda ake biyansa.

Daga cikin 'yan wasan da suke wasa a kungiyoyin Najeriya akwai 'yan wasa daga kasar Brazil da ake ganin ta fi kowace kasa fice da kwarewa a harkar tamaula, da kuma koci shi ma daga Brazil.

Ga kadan daga cikinsu:

1. Fatau Daudu daga Ghana

Fatau Daudu mai shekara 33, wanda asalin sunansa shi ne Abdulfatawu Daudu, dan asalin kasar Ghana ne.

Asalin hoton, Ghanafans.com

Bayanan hoto,

Golan kungiyar Enyimba Fatau Daudu dan Ghana ne

An haife shi a garin Obuasi, kuma yanzu haka shi ne golan kungiyar Enyimba ta Aba da ke jihar Abia.

Ya zuwa yanzu, Fatau ya kama wa kasar Ghana wasa 25, kuma a shekarar 2016 ne Enyimba ta dauko shi daga kungiyar Ashanti Gold ta Ghana.

2. Yaya Kone daga Cote d'Ivoire

Yaya Kone dan asalin kasar Cote d'Ivoire ne kuma an haife shi a garin Dodougnoa.

Yanzu haka yana da kimanin shekara 20.

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Yaya yana wasa ne da Lobi Stars ta Makurdi ne da ke jihar Benue

Yana tare da kungiyar Lobi Stars ta Makurdi ne da ke jihar Benue, wanda kuma wannan ne karo na biyu da yake kasancewa tare da su.

A shekarar 2015 ne kungiyar Lobi Stars ta dauko Yaya Kone daga kungiyar AS Denguélé da ke kasar Cote d'Ivoire.

Bayan kakar 2015, sai ta sayar da shi ga kungiyar Ifeanyi Ubah domin kakar 2016, sannan kuma a watan Nuwamban bara Lobi ta sake dauko shi daga Ifeanyi Ubah domin kakar bana.

A kakar bara, Yaya ya zura wa kungiyar Plateau United kwallo uku rigis (Hatrick) a wani wasa mai zafi tsakaninsu.

Yanzu ya buga wa kungiya biyu ke nan a Najeriya daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Yanzu haka Yaya Kone yana cikin 'yan wasan da suka fi zura kwallaye a gasar firimiyar ta bana, inda yake da kwallo biyu a wasa biyar.

3. Jean Efala daga Kamaru

Asalin hoton, 234football

Bayanan hoto,

Jean Efala daga Kamaru yana taka leda ne a kungiyar Akwa United

Jean Efala dan asalin kasar Kamaru, kuma yana daya daga matasan gololin kasar masu tashe wadanda ake sa ran wata rana za su kare martabar kasar a fagen kwallon kafa.

Yanzu haka Jean Efala golan kungiyar Akwa United ne da ke jihar Akwa Ibom.

Kafin zuwansa Najeriya ya yi kwallo a kungiyoyin Fovu Baham da Coton Sports da Colombe Sangmelima duk a kasar Kamaru.

A bangaren buga wa kasarsa kuwa, Jean ya kama wa Kamaru a tawagar 'yan wasan kasa da shekara 17 da 'yan kasa da shekara 20, inda ya wakilci a gasar cin kofin duniya.

4. Alberico Barbosa Da Silva daga Brazil

Asalin hoton, Twitter/@realbassey

Bayanan hoto,

Alberico ya taba buga wa kungiyoyin Vera Cruz da Guarani da Decisao duka a Brazil

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Alberico Barbosa Da Silva dan kasar Brazil wanda yanzu haka yake tare da kungiyar Akwa United ta jihar Akwa Ibom.

Alberico dan wasan tsakiya ne, wanda daga kallon wasansa, babu shakka za ka gane cewa akwai iyawa a tare da shi.

Akwa United ce kungiya ta biyu da ya buga wa kwallo a Najeriya bayan ya kasance a kungiyar Ifeanyi Ubah a kakar bara.

Ya buga wa kungiyoyin Vera Cruz da Guarani da Decisao duka a Brazil kafin ya dawo Najeriya da taka leda.

A bangaren buga wa gida wato kasarsa Brazil kuwa, Alberico ya buga wa tawagar kasar ta shekara 17, inda har ya zura kwallo hudu a wasanni 16 da ya buga.

5. Rafael Everton daga Brazil

Baya ga 'yan wasa da suke tururuwa zuwa Najeriya, Rafael Everton mai horar da 'yan wasa ne daga kasar Brazil da yanzu haka yake horar da kungiyar Akwa United.

Kafin zuwansa Akwa United, Rafael ya horar da kungiyar Fluminense FC na Brazil da kungiyoyin Ifeanyi Ubah da Abia Warriors.

6. Drissa Bamba daga Cote d'Ivoire

Asalin hoton, Brila.net

Bayanan hoto,

Drissa Bamba ya koma kungiyar Ifeanyi Ubah ne a shekarar 2016

Drissa Bamba, golan Rivers United ne daga kasar Cote d'Ivoire.

Ya fara dira kungiyar Ifeanyi Ubah ce a shekarar 2016 bayan ta sayo shi daga kungiyar Stade d'Abidjan da ke birnin Abdijan na kasar Cote d'Ivoire.

A bana ne ya koma kungiyar Rivers United da ke jihar Rivers domin maye gurbin tsohon golansu, kuma tsohon golan Super Eagles, Rotimi Sunday.

7. Jean Marie Guera daga Jamhuriyar Benin

Dan asalin kasar Jamhuriyar Benin, yana taka leda a kungiyar Enyimba da ke jihar Abia a yanzu haka.

8. Faruk Mohammed daga Ghana

Dan kasar Ghana ne da yanzu haka shi ma yake kungiyar Enyimba.

9. Nana Bonsu daga Ghana

Golan Enugu Rangers wanda shi ma dan kasar Ghana ne.

10. Papa Ousmane Sane daga Senegal

Dan kasar Senegal ne da ke kungiyar Rangers ta jihar Inugu.