Kun san yawan kudin da Google ya samu a karshen 2018?

Kamfanin Alphabet wanda shi ne ya mallaki kamfanonin Google da YouTube da kuma kamfanin salula na Android ya sanar da cewa ya sami bunkasa ta fannin hada-hadar kasuwanci.
Bayanan sakamakon kasuwancin sun ta'allaka ne a watanni uku na karshen shekarar 2018.
Amma masu zuba jari a kamfanin na dari-dari da hannayen jarin kamfanin saboda rashin cimma matakin da aka yi hasashen hannun jarin kamfanin zai yi.
Kamfanin ya sami bunkasa musamman a fannin tallace-tallace ta intanet, fagen da shi ke kan gaba a duniya, inda ya sami fiye da dala biliyan 39.
Wannan ya zama karuwar kashi 22 cikin 100 kenan idan aka kwatanta da abin da ya samu a watanni uku na karshen shekarar 2017.
Yawancin kudaden dsa kamfanin na Alphabet ya samu sun fito ne daga tallace-tallace da sashin kamfanin na Google ya samar - kimanin dala biliyan 32 da miliyan 600.
Amma kamfanin na kara kashe kudade masu yawa wajen inganta wannan sashin nasa mai kula da talace-tallace.
Kudaden da kamfanin ya kashe a wannan fannin ya zarce dala biliyan 7 a watanni uku na karshen shekarar ta bara, wanda ke nuna karuwar kusan dala biliyan daya idan aka kwatanta da abin da ya kashe a bara.
Amma duk da haka, masu zuba jari a kamfanin sun tsorata da rashin karsashin da hannun jarin kamfanin ke nunawa.
Lamarin da ya sanya farashin hannun jarin kamfanin na Alphabet ya fadi da kashi 2 cikin 100 jim kadan bayan an bude kasuwannin hannayen jari.