Ku kalli hotunan ziyarar Atiku a Kano

Dandazon jama'a a filin wasan
Image caption Dandazon jama'a a filin wasan

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyarar yakin neman zabensa a Kano.

Tuni Atiku ya isa Kano daya daga cikin jihohin da ke tantance makomar zaben shugaban kasa a Najeriya.

Dan takarar na PDP ya fara kai ziyara ne fadar mai martaba Sarkin Kano kafin isa filin gangamin yakin neman zabensa

Mutane da dama ne suka cika makil a taron siyasar na Atiku a filin kwallon kafa na Sani Abacha a Kano.

Wasu daga cikin 'yan wasan kwaikwayo na hausa kamar Sani Danja da Adam Zango wanda ya sauya sheka ba da dadewa ba, na cikin tawagar Atiku a Kano

Image caption Wasu mutane na zaman zuwan dan takarar