Zaben cancanta za ayi a Najeriya -— Babangida

Ibrahim Badamasi Babangida Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ibrahim Badamasi Babangida

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya bukaci jama'a da su yi amfani da hankalinsu wajen zaben shugabannin da za su kawo zaman lafiya mai dorewa a kasar.

A wata hira da ya yi da BBC, Janar Babangida, wanda ke cewa ya na cikin koshin lafiya, ya ce ba shi da fatan da ya wuce na ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali.

Ya ce 'yan takara sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan zabe, kuma ya na fatan kowanne bangare zai mutunta hakan da kuma gujewa musayar bakaken kalamai.

Janar Babangida, ya ce babu wanda ya ke goyon-baya ko zai umarci 'yan kasar su zaba sai dai ya na fatan a yi zabi nagari.

Tsohon shugaban ya kuma ce, yanzu kan mutane ya waye, kowa ya san 'yanci don haka baya ji a yanzu za iya amfani da kudi wajen sayen kuri'a don haka yana da yakinin cewa za ayi zabe bisa ga cancanta.

A kan batun matasa kuma a harkar siyasa, ya ce alamomi da adadin matasa da ake gwagwarmaya da su a yanzu, sun nuna cewa nan gaba za su lakanci komai, kuma suma mata sannu a hankali za su yi rawar gani.

Kwana biyar kacal ya rage a soma babban zaben Najeriya inda za a fafata takarar shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP.