MDD ta soki Buhari kan Onnoghen

Shugaba Buhari na neman wa'adi na biyu ne a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Buhari na neman wa'adi na biyu ne a Najeriya

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce shugaban Najeriya ya karya dokoki a lokacin da ya dakatar da Babban Alkalin kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Walter Onnoghen cikin watan jiya bisa zarge-zargen kin bayyana kadarorinsa.

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan 'yancin alkalai da lauyoyi, Diego Garcia-Sayan ya ce ya kamata a ce kotu ce za ta dauki irin wannan matakin da shugaban ya dauka.

Ya ce korar alkalai ba tare da bin matakan shari'a ba, bai dace da 'yancin kotuna ba.

A watan da ya gabata ne shugaban kasar ya dakatar da Mista Onnoghen bisa shawarar kotun da'ar ma'aikata wacce ta samu alkalin alkalan da laifin kin bayyana cikakkun kaddarorinsa lokacin da aka nada shi kan mukamin a 2017.

Sai dai Mista Onnoghen ya ce ba da gangan ya yi hakan ba, yana mai cewa mantawa ya yi.

Dakatar da Babban Alkalin dai ya jawo suka daga kasashen duniya.

A matsayinsa na babban alkalin Najeriya, zai taka muhimmiyar rawa a duk wani rikici da ka iya tasowa a zabukan da za a yi wannan makon.