Malaman jami'a sun shiga zanga-zanga a Sudan

Men in a pickup truck Hakkin mallakar hoto Protester

Jami'an tsaro a Sudan sun tsare wasu malaman jami'a da ke zanga-zanga a Khartoum, babban birnin kasar.

Likitoci da dama sun fito suna zanga-zanga a asibitoci inda suke kira da shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa, kuma tun watan Disambar bara jama'ar kasar ke karawa da jami'an tsaro.

Kungiyar Human Rights Watch mai fafutukar kare hakkin bil Adama ta ce jami'an tsaro sun kashe akalla mutum 50.

Ba kamar yadda aka saba gani a wasu sassa na nahiyar Afirka ba - inda yawancin masu fita zanga-zangar adawa da gwamnati kan kasance matasa marasa aikin yi ne.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Omar al-Bashir ya mulki Sudan tun 1989

Amma a Sudan likitoci maza da mata da malaman makaranta da sauran ma'aikata ne ke fuskantar harsasai da hayaki mai sa hawaye da kuma kulakan 'yan sandan gwamnatin Shugaba Omar al Bashir.

'Yan sa'o'i kadan da suka gabata an kame wasu malaman jami'a a birnin Khartoum.

An kuma gabatar da wasu jerin zanga-zanga a asibitoci goma cikin babban birnin kasar - an kuma bukaci Shugaba Omar al Bashir ya sauka daga mukaminsa.

Mako biyu da ya gabata gwamnatin Sudan ta ce za ta saki dukkan wadanda ta damke sakamakon zanga-zangar da aka shafe fiye da wata biyu ana yi a fadin kasar.

Amma yawancin wadanda ke tsaren ba su sami 'yancinsu ba.

Masu rajin kare hakkin dan Adam a Sudan na fargabar cewa gwamnati na iya kama su domin gwamnatin kasar na tsare da mutane masu yawa a wurare na sirri.

Suna kuma tsorn jami'an tsaron na iya gallaza masu azaba.

Labarai masu alaka