Amurka na son mika wa Saudiyya fasahar nukiliya a asirce

President Trump at the Arab Islamic American Summit in Riyadh in 2017

Asalin hoton, MANDEL NGAN VIA GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Shugaba Trump a wajen taron koli tsakanin Amurka da Larabawa a Riyadh a 2017.

Wani rahoton da majalisar kasar Amurka ta fitar ya fallasa yadda kasar ke rububin sayar wa Saudiyya fasahar kimiyyar nukiliya.

Majalisar Wakilai da ke karkashin jam'iyyar adawa ta Democrat ce ta kaddamar da wani bincike kan damuwar da ta bayyana cewa Fadar White House na son gina wasu tashoshin samar da makamashin nukiliya a wurare daban-daban cikin daular ta Saudiyya.

Binciken ya kuma gano cewa wasu kamfanoni da ke da alaka da Shugaba Donald Trump ne ke kan gaba wajen sayar wa Saudiyyar fasahar, lamarin da ka iya rikita siyasar Gabas ta Tsakiya.

Fadar White House ta ki cewa uffan game da sakamakon wannan binciken.

Rahoton kwamitin da ke sa ido na majalisar wakilan Amurka ya fallasa cewa cikakken bincike kan lamarin ya zama wajibi saboda hatsarin da ke tattare da kokarin na Amurka na sayar wa Saudiyya fasahar nukiliya.

An kuma gano cewa Shugaba Trump ya yi wata ganawa da wasu kamfanoni masu kera tashoshin nukiliya a Fadar White ran 12 ga wannan watan, kuma Saudiyya na cikin kasashen Gabas ta Tsakiya da suka halarci taron.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Surukin Mista Trump, Jared Kushner (dama)

Sannan surukin Mista Trump, Jared Kushner zai kai wata ziyara yankin a wannan watan domin tattauna kudin da gwamnatin Mista Trump ke bukata wasu kasashen yankin su biya.

Rahoton kuma na dubawa ya ga idan wannan yunkurin na Mista Trump zai taimakawa Amurka ne ko kuma wasu tsirarun mutane da ke da alaka da shugaban kansa za su azurta.

Dukkan 'yan manyan jam'iyyun na tsoron matakin na Mista Trump na iya tayar da wani rikici na rige-rigen mallakar makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya, musamman daga abokan hamayyar Saudiyya kamar Iran.