An daure mai fasa kwaurin hauren giwa shekara 15 a Tanzania

Yang Fenglan was a leading figure in business circles at the time of her arrest

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Sarauniyar Hauren Giwa' Yang Fenglan

Wata kotu a Tanzaniya ta yanke wa wata mata 'yar China hukunci saboda fasa kwauri da safarar hauren giwa.

Yang Fenglan ta yi kaurin suna, har ana kiranta Sarauniyar Hauren Giwa.

Hukumomin kasar sun ce matar ce jagorar masu safarar hauren giwa a nahiyar Afirka a cikin shekara fiye da goma da ta gabata, kuma sun ce ta sami miliyoyin dalolin Amurka a wannan haramtaccen ciniki na farautar giwaye daga Afirka zuwa China da yankin Gabas mai nisa.

An dai kiyasta cewa sarauniyar hauren giwar ta yi fasa kwaurin hauren giwaye fiye 350

A yayin da aka kama ta a shekara 2015, masu fafutukar kare yanayi sun ce a karshe an kama daya daga cikin manyan masu fasa kwaurin haramtaccen cinikin hauren giwa.

Yanzu wata kotu ta same ta da laifi, kuma ta yanke ma ta hukuncin shekara 15 a gidan yari. Gwamnatin kasar kuma za ta kwace dukkan kaddarorinta da kamfanonin da ta mallaka.

Masana na cewa ana samun raguwar giwaye a duniya saboda ayyukan masu farautarsu, kuma wannan ya sanya giwayen suka shiga cikin dabbobin dawa da ake gain za su iya karewa gaba daya daga doron kasa idan ba a dauki matakin kare su ba.

An dai kiyasta cewa nahiyar Afirka ta rasa kimanin kashi 90 cikin 100 na giwayenta cikin shekara 100 da ta gabata, yadda a yanzu saura kimanin giwaye 400,000 kawai suka rage.