An kashe fiye da mutum 130 a Kajuru - El-Rufai

An kashe fiye da mutum 130 a Kajuru - El-Rufai

Sai ku latsa alamar lasifika domin jin kalaman Gwamna El-Rufai.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce adadin mutanen da aka kashe a wasu hare-hare da aka kai kan rugagen Fulani a karamar hukumar Kajuru ya haura mutum 130 yanzu.

A makon jiya gwamnan ya ce an kashe mutane 66 ne a wajen inda wasu mutane ke ganin ya zuzuta alkaluman ne.

Sai dai da yake yiwa manema labarai bayani, bayan kammala wani taro kan tsaro da shugaba Muhammadu Buhari, Gwamna El-Rufai ya ce suna da hotuna da kuma jerin sunayen wadanda aka kashen.