Mazauna Buni Yadi: A garinmu za mu yi zaben 2019

Mazauna Buni Yadi: A garinmu za mu yi zaben 2019

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron bayanan nasu:

Wasu mazauna garin Buni Yadi na jihar Yobe da mayakan Boko Haram suka kai hari a ranar Asabar da ta gabata, sun ce a shirye suke su fito su jefa kuri'a a zaben a ranar Asabar mai zuwa.

Rundunar sojan Najeriya ta ce mayakan sun kashe sojoji hudu, aka kuma kashe 'yan Boko Haram 5 a lokacin da suka yi kokarin kwace iko da garin.

Kawo yanzu dai hukumar zaben kasar INEC ba ta ce ko za a gudanar da zabe a yankin ba a ranar Asabar mai zuwa.

Ga ra'ayoyin wasu mazauna garin na Buni Yadi da wakilinmu na wucin-gadi a jihar Yobe Muhammad Garundole ya ttatro mana.