Za a kulle attajirin Indiya Anil Ambani saboda bashin $77.39 mn

Anil Ambani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Attajiri Anil Ambani

Attajirin nan dan kasar Indiya Anil Ambani na fuskantar dauri a gidan yari saboda bashin da kamfanin Ericsson ke bin kamfaninsa RCom.

Wannan ya biyo bayan rushewar wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kamfanin nasa Reliance Communications (RCom) da babban kamfanin sadarwa na Ericsson.

Kamfanin Ericsson na neman RCom ya biya shi kusa dala miliyan 77 na wasu kudade da Rcom din ya gaza biyansa, kuma ya shigar da karar neman hakkinsa.

Kotun da ta yanke hukunci a wannan karar ta gargadi Mista Ambani cewa za ta daure shi a gidan yari idan bai biya dukkan kudaden ba cikin mako hudu.

Kamfanin Ericsson ya sanya hannu kan yarjejeniyar a 2014, kuma ya kai karar RCom a bara.

Kotun ta gano cewa shugaban kamfanin RCom, Satish Seth da shugaban Reliance Infratel Chhya Virani suna da hannu wajen karya yarjejeniyar.

Amma dukkansu na iya kaucewa hukuncin kotu idan aka biya dukkan kudin har da kudin ruwa da ya hau kai.

Asalin hoton, THE BRIDAL BOX

Bayanan hoto,

Anil Ambani da matarsa tsohuwar tauraruwar Bollywood Tina Munim

A daya bangaren kuma, kamfanin Reliance Industries, wanda Mukesh Ambani ke jagoranta na tattaunawa da kamfanin Saudi Aramco domin zuba jari a Indiya.

Kamfanin mai na Saudi Aramco ya kulla wata yarjejeniya a watan Afrilu da wasu kamfanonin tace man fetur na Indiya domin kafa wata sabuwar matatar mai da darajarta ya kai dala biliyan 44.