'Yan matan kungiyar IS na tsaka mai wuya

Hoda da Shamima
Bayanan hoto,

Shamima Begum (dama) Hoda Muthana

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai amince wata mata mai suna Hoda Muthana da ta bar Amurka domin yi wa kungiyar IS aiki ba komawa kasar ba.

Shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter cewa ya umarci sakataren harkokin waje na Amurka Mike Pompeo ya hana matar mai suna Hoda Muthana shiga cikin kasar.

Wannan rahoton ya yi kama da na wata 'yar Birtaniya da ita ma ta shiga kungiyar IS amma yanzu tana son komawa gida, matakin da Birtaniyar ta ki amincewa da shi.

Mista Pompeo ya ce matar mai shekara 24 da haihuwa ba 'yar Amurka ce ba, saboda haka ba za a bar ta ta shiga kasar ba.

Amma 'yan uwanta da lauyanta sun kafe cewa Moda 'yar Amurka ce.

Hoda Muthana ta girma a jihar Alabama ne, kuma daga can ta tafi Syria domin shiga kungiyar IS a lokacin tana da shekara 20 da haihuwa.

Amma ta yi wa 'yan uwanta karyar cewa za ta tafi wani taro na jami'arsu ne a Turkiyya.

Wannan lamarin ya yi kama da na wata matar 'yar Birtaniya mai suna Shamima Begum wadda tuni kasarta ta kore ta, kuma ta hana ta komawa Birtaniya gaba daya.

Ita ma Shamima Begum na fafutukar komawa London, kamar yadda Hoda Muthana ke son komawa Amurka.

Miss Muthana na jariri mai shekara daya da rabi, kuma ta ce tayi nadamar shiga kungiyar ta IS.

Hoda da Shamima na cikin daruruwan 'yan mata da suka bar kasashensu na yammacin Turai domin shiga kungiyar IS, amma yanzu da aka fatattaki kungiyar, sun kasance ba su da wurin zuwa.