Mufti Menk ya taya Buhari murnar lashe zaben 2019

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Malamin ya taba ziyartar Shugaba Buhari a Abuja a shekarar 2018

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan Mufti Menk ya taya Shugaba Buhari murnar lashe zaben 2019.

Malamin wanda dan asalin kasar Zimbabwe ne ya yi fatan Allah "ya kare shugaban, ya kuma ci gaba da yi masa jagora a dukkan al'amuransa."

A ranar Larabe ne aka bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.

Shugaban mai shekara 76, na jam'iyyar APC, ya kayar da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri'u kusan miliyan hudu.

Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP, wacce Atiku ya yi wa takara, ta yi watsi da sakamakon zaben da Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Mahmood Yakubu ya bayyana da misalin karfe 4.30 na asuba.