Abiy Ahmed ya sasanta Somaliya da Kenya

The Ethiopian prime minister Abiy Ahmed helped mediate between the presidents of Somalia and Kenya Hakkin mallakar hoto Ethiopia's Prime Minister's Office
Image caption Firai ministan Habasha Abiy Ahmed ya taimaka wajen sasanta shugabannin Somaliya da Kenya

Kenya da Somaliya sun mayar da dangantakar diflomasiya bayan wata matsala kan mallakar wasu rijiyoyin mai da ke cikin teku.

Firai ministan Habasha Abiy Ahmed ne ya shiga tsakani, inda shugabannin Somaliyan da Kenya suka gana da juna kai tsaye kan batun a Nairobi.

A watan jiya ne dai Kenya ta kori jakadan Somaliya daga kasarta bayan da rahotanni suka fito cewa Somaliyar na sayar da wasu daga cikin rijiyoyin man da ke yankin da suka dade suna takardama a kai.

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ne ya karbi bakuncin takwaransa na Somaliya Mohamed Farmajo a Nairobi, domin samar da mafita kan mallakin yankin gabar tekun Indiya da masana suka ce yana da albarkatun man fetur da gas mai tarin yawa.

Wannan rikicin dai ya samo asali ne bayan da 'yan siyasar kasar Somaliya suka zargi gwamnatinsu da kokarin sayar da wasu rijiyoyin mai a yankin, batun da ya tayar da hankalin gwamnatin Kenya.

Da Kenya ta fahimci Somaliya ta kira wani taro kan batun a birnin Landan, sai ta fusata, inda ta ce ba za ta amince da dukkan wani mataki da Somaliya za ta dauka ba kan batun.

Tun da farko, Somaliya ta kai karar Kenya a kotun kasa da kasa kan batun da kawo yanzu ba ta yanke hukunci ba.

Sasantawar da kasashen suka yi zai taimaka wa kokarin yakin da ta'addanci da ya addabi yankin.

Kenya na da fiye da dakaru 4,000 a Somaliya wadanda ke cikin tawagar dakarun Tarayyar Afirka masu yaki da mayakan kungiyar al-Shabab.

Labarai masu alaka