Guguwar Idai: Mutane da dama sun mutu a Zimbabwe da Mozambique

Destruction in Mozambique Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ba shi ne karon farko da Mozambique ke fuskantar irin wannan iftila'i ba

Wata guguwa da ke tafe da ruwan sama kamar da bakin kwarya ta karya gadoji da lalata gidaje a gabashin Zimbabwe, tare da kashe akalla mutum 24.

Guguwar da aka bayyana da Cyclone Idai ta katse layukan sadarwa da wutan lantarki a wasu yankunan lardin Manicaland da ke da iyaka da Mozambique. Mutum 40 sun bata.

Mutane sun kauracewa gidajensu zuwa yankunan da ke da tsauninka inda suke jiran a kai musu dauki, sai dai iskar da ake mai karfi ta hana jirage masu saukan angulu isa gare su.

A Mozambique, inda guguwar Idai ta rusa gidaje a ranar Alhamis, akalla mutum 19 ta kashe.

Ambaliyar ruwa a sauran sassan kasar ta kuma kashe mutum kusan 70 kafin isowar guguwar

Ma'aikatar sadarwar Zimbabwe ta ce an dau matakan raba garin Chimanimani da sauran yankunan lardin Manicaland. Dakarun sojin kasar na jagorantar aikin ceto a cewar ta.

Akwai yiwuwar a samu karuwar alkaluman mamata, yayin da mahukunta ke fafutikar ganin sun isa yankunan da abin ya shafa.

Kakakin Jam'iyyar adawa ta Movement for Democratic Change, Jacob Mafume, ya ce al'ummar gabashin kasar sun fada a cikin yanayi na hau'u'la'i.

Mozambique ta sha fuskantar irin wadanan iftila'i na guguwa, a shekara ta 2000 ta fuskancin guguwar Eline da ta kashe mutum 350 da raba mutum 650,000 da matsugunai.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gidajen da guguwa ta ruguza a Mozambique

Yankin Beira na yawan fuskantar ruwan sama mai karfi, wannan dalili ne ya sa aka yi kokarin bijiro da dabarun rage adadin cikowar ruwa a teku wanda sauyin yanayi ke haifarwa.

Labarai masu alaka

Karin bayani