Zaben Kano: 'Mun yi mamakin soke zaben gundumarmu'

A ranar 23 ne INEC za ta sake gudanar da zaben gwamna a Kano da wasu jihohin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayan kammala zaben gwamnoni a Najeriya, sakamakon mazabar Gama da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano na daga cikin wadanda aka soke.

Kuma tana daga cikin mazabun da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce za a sake gudanar da zabe a cikinta, kafin bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.

BBC ta je wannan unguwa, inda ta tattauna da wasu daga cikin mazauna unguwar dangane da soke zaben gundumar.

Daya daga cikin mazauna unguwar mai suna Shehu Hussain, ya ce sun yi mamakin yadda a aka soke zaben gundumar.

Ya ce 'wannan zabe da aka soke ya zo mana da ba-zata, domin ba mu taba zaton za a soke zaben Gama ba.'

Ya kuma yi ikirarin cewa babu inda aka samu rikici a yankin na Gama a lokacin zaben na gwamna wanda ya gudana a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

A halin yanzu dai al'ummar yankin na Gama sun ce suna yin tarurruka tsakanin su domin tabbatar da ganin an yi zaben da aka ce za a sake cikin lumana.

An dai samu rahotanni na yunkurin sayen kuri'a a gundumar ta Gama, inda jami'an 'yan sanda suka tabbatar da cewa sun kama wasu mutane da ake zargi da sayen katunan zabe daga hannun al'umma.

Baya ga Kano, sauran jihohi da za a sake zabe a cikin su su ne Adamawa da Filato da Sokoto da kuma Binuwai.