Mali ta dakatar da kungiyar mafarauta saboda kisan mutum 134

Fulani na sana'ar kiwo ne a Mali Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fulani na sana'ar kiwo ne a Mali kamar sauran

Shugaban Mali Boubacar Keita ya kori babban kwamandan sojojin kasar kwana daya bayan da wasu 'yan kabilar Dogon suka kashe wasu Fulani fiye da 130 a kauyensu, da ke yankin Mopti na kasar.

Gwamnati ta kuma ce za ta haramta wata kungiyar 'yan sa kai da ta ce ke da alhakin kai harin.

Da sanyin safiyar ranar Asabar ne wasu mahara 'yan wata kungiyar mai suna Dan na Ambassagou da ke dauke da bindigogi suka afka wa wani kauyen Fulani da ke yankin Mopti na kasar Mali, inda suka hallaka fiye da mutum 130.

Mafarauntan na zargi sojoji kasar da gazawa wajen kare su daga hare-haren da suka ce kungiyoyin 'yan jihadi ke kai masu, kuma sun ce wasu daga cikin 'yan kabilar Fulani na da alaka da kungiyoyin ta'addanci a cikin kasar.

n dai dade ana samun irin wannan rikicin tsakanin mafarauta 'yan kabilar Dogon da Fulani makiyaya akan iko da filayen noma da na kiwon dabbobi.

A nasu bangaren Fulanin na cewa sojojin kasar ne suke horar da 'yan kabilar ta Dogon kuma suna ba su makamai domin su kai wa 'yan kabilar Fulani hari, matakin da sojojin kasar suka dade suna musantawa.

Jim kadan bayan kai wannan harin, gwamnatin Mali ta haramta kungiyar mafarautar da ta kai harin, kuma ta sanar da ta kori manyan kwamandojin sojojin kasar, inda ta maye gurbinsu da wasu sabbin kwamandoji.

Labarai masu alaka