Rarara: Karin bayani kan wakar 'ta leko ta labe'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kahutu Rarara: 'Abin da ya sa na yi wakar 'Ta leko ta labe'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hirarmu da Rarara.

Fitaccen mawakin siyasar nan a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da dan takarar jam'iyyar APC a Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samu na lashe zaben jihar.

A hirar da BBC ta yi da mawakin, ya yi bayani kan wasu kalamai da ya yi amfani da su a wakokinsa da ya yi wa Gwamna Ganduje.