Syria na neman kai da mayakan ISIS

Karbo ikon Baghuz abu ne mai muhimmanci a yaki da kungiyar IS Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yankin Baghuz yanki ne mai muhimmanci a yaki da kungiyar IS

Gwamnatin yankin Kurdawa a Syria ta yi kira da a kafa wata koun kasa da kasa domin hukunta wadanda ake tuhuma da zam 'yan kungiyar IS.

Gwamnatin ta ce ba ta ji dadin yadda sauran kasashen duniya ke shiriritar da batun abin da ya kamata a yi da mayakan kungiyar ba. Akwai dai daruruwan 'yan kasashen waje a cikin wadanda ake tsare da su a yankin.

Gwamnatin yankin Kurdawa a cikin syria ta ce tana tsaka mai wuya game da batun duban mayakan kungiyar IS da 'iyalansu da aka fatattaka daga wuri na karshe da suka ja daga.

Shugaban ma'aikatar harkokin waje na yankin Abdul Karim Umar ya sanar da BBC cewa kasashen da suka mayar da mayakan kasashensu na asali ba su da yawa, kuma yawan mayakan na karawa gwamnatin wani nauyi da ba za ta iya dauka ba.

Ya ce ko aikin tsare su na so ya gagari gwamnatin ma, balle yi masu shari'a.

Da alama wannan kiran na a kafa wata kotun kasa da kasa wani kokari ne gwamnatin yankin Kurdawan ke yi domin magance matsalar wasu daga cikin mayakan tserewa a yankin da har yanzu al'amuran tsaro ba su daidaita ba.

Labarai masu alaka