Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Allah ne ya ba mu wannan nasarar – Abdullahi Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce zaben da ya sami galaba a kan Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP daga Allah lamarin ya ke.

Gwamnan ya gode wa al'ummar jihar Kano da kamar yadda ya ce "Suka fito da yawansu suka zabe ni".

Ya kuma nemi hadin kan sauran wadanda suka yi takara da shi domin cigaban Kano.

Sai ku latsa hoton da ke sama domin jin hirar da BBC ta yi da gwamnan da kuma martanin da ya mayar wa masu cewa an murde zaben ne.