Manoma sun yi asarar dukkan amfanin gonarsu a Mozambique

Many of those affected are subsistence farmers

Asalin hoton, EPA

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mahaukaciyar guguwar nan da ta daidaita yankunan kasashen Mozambique da Malawi da kuma Zimbabwe ta yi sanadiyyar rasa amfanin gona na kwatankwacin shekara guda.

Hukumar ta yi wannan gargadin ne a lokacin da ake ci gaba da kokarin kai taimakon abinci da magani ga dubban daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa ta mamaye yankunansu gaba daya.

Shugaban hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, David Beasley ya ce kusan mutum 250,000 ne ke bukatar muhalli, kuma suna bukatar taimakon gaggawa ne babu bata lokaci.

Amma ya ce manoma a yankin sun yi asarar dukkan abin da suka noma a bana.

Yankin Beira na kasar Mozambique shi ne wanda wannan matsalar ta fi shafa, domin ambaliyar ruwa da ta biyo bayan mahaukaciyar guguwar ta shafe dukkan gonakin yankin, lamarin da ya lalata dukkan abin da manoman suka shuka.

Noma dai shi ne babban abin da yawancin mutanen yankin suka dogara da shi, kuma babu wanda ya san yawan asarar da kasashen da wannan ibtila'i ya auka ma sai bayan ruwan ya janye.