Sanya matsattsen wando na mata ya jawo surutu a jami'a

wasu mata sanye da matsattsen wando Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yanzu mata ba sai a wajen motsa jiki suke sa matsattsen wando ba

Wata wasika da wata uwa ta rubuta saboda damuwar da ta yi kan yadda 'yan mata dalibai suke sanya matsattsen wando mai bayyana siffar jiki (leggings) a wata jami'a a birnin Indiana na Amurka ta jawo surutai da harzuka mata.

A wasikar wadda aka sanya a mujallar daliban jami'ar wadda matar mai suna Maryann White ta rubuta, ta ce: '' Ni uwa ce 'yar darikar Katolika mai 'ya'ya maza hudu, da nake da wata matsala wadda mata ne kawai za su iya magancewa: matsalar ita ce, matsattsen wando.''

Matar ta yi bayanin cewa, ganin yadda 'yan mata dalibai kusan kowacce ke sanye da matsattsen wando, a lokacin da ta ziyarci 'ya'yanta maza hudu a makarantar ta ce abin ya ba ta takaici, saboda da wuya samari maza su iya kawar da ido daga kallon jikin mata.

Matar ta bayar da shawara ga dalibai mata na jamia'r ta Notre Dame, da cewa, kamata ya yi nan gaba idan suka je kanti sayen wando su yi tunanin iyayen dalibai mazan, su sayi wandon jins (jeans), maimakon matsattsun wanduna masu bayyana siffar jiki.

Ba tare da wata-wata ba, sai kawai 'yan matan jami'ar suka rika mayar da martani a kan wannan wasika ta uwar.

Wasu daga cikin 'yan matan sun ce suturar da za su sa zabinsu ce, saboda haka bai kamata a sa mu su ido ba, a bar mata kawai su sanya duk abin da suke so.

Wata kungiyar dalibai mai suna, "Irish 4 Reproductive Health" a jami'ar har shirya biki ta yi na ranar sanya irin wannan matsattsen wando, domin karfafa wa kowa da kowa maza da mata sanya irin wandon a jami'ar.

Kungiyar ta yi hakan ne domin nuna kin yardarta da cewa mata ne ke janyo irin abin da maza kan yi musu, na cin zarafi, ko fyade, saboda irin shigar da matan kan yi.

Wasu daliban mata sun rika sanya hotunansu sanye da matsatten wandon, a shafukan intanet a matsayin alama ta kin yarda da maganar matar.

Hakkin mallakar hoto @anniejarr
Image caption Daya daga cikin daliban mata da ke alfahari da sanya matsattsen wandon

Sanya irin wannan wando ba wani abu ba ne a wurin wasu daliban mata a jami'ar, amma a dalilin maganar da ta taso sai wasu da ba su taba sanyawa ba su fito bainar jama'a suka rika yin hakan a karon farko.