An kama gwamna kan almundahana

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

An kama wani gwamna a kasar Kenya bisa zargin almundahana ta kusan dala 827,000 wato kusan miliyan 300 kenan a kudin Najeriya.

Kamen da aka yi wa gwamnan jihar Samburu, Moses Kasaine na zuwa ne bayan da babban mai shigar da kara Noordin Haji ya bayar da umarnin cewa a tuhumi gwamnan da cin amanar kasa da kuma amfani da ofishinsa domin biyan bukatar kansa.

Har yanzu Mista Kasaine da lauyoyinsa ba su ce komai kan lamarin ba.

A wata sanarwa da Mista Haji ya fitar, ya bayyana cewa Mista Kasaine ''ya yi ta amfani da jiharsa domin yin kasuwanci da kamfanin Oryx Service Station domin yin jigilar man fetur tun 27 ga watan Maris din 2013.''

Kamfanin man ya karbi kudade da suka kai dala 827,000 kusan miliyan 300 kenan a kudin Najeriya kuma an rarraba kudin ne tsakanin gwamnan da wasu wakilansa.

Mista Haji ya bayyana cewa Mista Kasaine bai fito fili ya bayyana dangantakar da ke tsakaninsa da kamfanin ba, kuma abinda ya aikata a yanzu ya sabawa dokar kasar.

Jihar Samburu dai na arewa da yankin Rift Valley na kasar Kenya.

Labarai masu alaka