Za a gina gidan zoo a barikokin soja a Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana dajin Sambisa a matsayin wajen da zai dace ta bude wurin yawon bude ido domin samun kudaden shiga.

Dajin Sambisa na daya daga cikin wuraren da 'yan kungiyar Boko Haram ke rawar gaban hantsi kafin sojojin kasar su kwace dajin a Disambar 2016 a cewarsu.

Shugaban rundunar sojojin kasar, Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana haka inda Manjo Janar Ali Nani ya wakilce shi a wajen taron gabatar da kasida mai taken ''Yaki da kalubalen da ake samu na tsaro dake da dangantaka da dazuzzuka da kuma killatattun wurare.''

Ya bayyana cewa an camfa cewa tarayya tsakanin sojoji da dabbobi na kawo sa'a.

Ya ce an kafa shirin nan na 'Barracks Investment Initiative Programme (BIIP)' domin taimakawa sojoji wajen noma da kiwo.

Buratai ya bukaci hukumomin da ke sa ido kan wuraren bude ido da su bayar da himma wajen tattalin wuraren bude ido da dazzuzuka kamar su dajin Kuyan Bana da Dajin Dan Sadau da Dajin Rugu da Dajin Gujba da dai sauransu.

Tun a bara ne dai Buratai ya bayyana aniyar mayar da dajin yankin Sambisa zuwa wurin yawon bude ido inda ya ce sojojin za su yi aiki tare da hukumar kula da wuraren yawon bude ido ta kasa domin ta taimaka wajan farfado da kimar dajin, domin masu yawon bude ido daga kasashen ketare su samu damar ganin namun daji.

Duk da cewa rundunar sojin kasar ta bayyana kwace dajin Sambisa daga hannun Kungiyar Boko Haram, har yanzu ana samun hare-hare daga kungiyar inda ake zargin daga cikin dajin Sambisar suke kitsa kai hare-haren.