Jirgin Ethiopia: Matukin ya kasa sarrafa jirgin

Masu Binciken hadarin jirgin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu Binciken hadarin jirgin

Rahotonnin farko na hadarin jirgin Ethiopia da aka samu sun nuna cewa jirgin ya yi ta yin tutsu a sama kafin ya fado kasa.

Matukin jirgin ya bi dukkan matakan da kamfanin ya yi umarni da a bi idan an hango matsala, kamar yadda rahotonnin farko na binciken da aka yi suka nuna.

Ministar zirga-zirga ta kasar Ethiopia Dagmawit Moges ta ce duk da kokarin da matukan jirgin suka yi ba su samu nasarar sarrafa jirgin ba.

Jirgin mai lamba ET302 ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha inda ya kashe mutum 157 da ke cikinsa.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Jirgi kirar Boeing 737 Max ya yi hadari a cikin watanni biyar.

Ko a watan Oktoban bara ma wani jirgin mai lamba JT 610 ya fadi a cikin wani teku kusa da kasar Indonesia, inda ya kashe duka mutane 189 da ke cikinsa.

A wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin Addis Ababa, Misis Dagmawit ta ce "Matukan sun bi duka matakan da kamfanin ya tanadar idan irin hakan ta faru, amma kuma ba su samu nasarar sarrafa jirgin ba."

An dai dakatar da tashin jirage mallakar kamfanin na Boeing 737 Max bayan hadarin na jirgin Ethiopia, lamarin da ya shafi akalla jirage 300.

Rahotonnin farkon dai ba su dora alhakin faduwar jirgin a kan kowa ba, haka kuma ba su bayar da cikakken bayani ba.

Sai dai kuma rohotonnin sun ce ya kamata kamfanin na Boeing ya sake nazarin matakan magance aukuwar hadari, sannan kuma dole ne hukumomin da ke kula da sufurin jiragen sama su tabbatar da cewa an magance matsalar kafin a kyale jiragen kamfanin su koma tashi.

Tun bayan aukuwar hadarin dai kamfanin ya dauki wasu matakai domin kare aukuwar irin hakan a nan gaba da suka hada da taimaka wa matuka kan yadda za su sarrafa jirgi yayin aukuwar hadari.