'Yan Najeriya sun harzuka kan kashe-kashen Zamfara

Masu zanga-zanga a a jihar Kaduna Hakkin mallakar hoto @Rjay_omale
Image caption Maza mata da kananan yara sun fito zanga-zangar a jihar Kaduna

Daruruwan 'yan Najeriya ne suka fita kan tituna a wasu jihohi na kasar da ma Abuja, inda suke yin maci don nuna fushinsu da damuwarsu kan kashe mutane da ake yi a jihar Zamfara.

A ranar Asabar ne al'ummar kasar suka fita rike da kyallaye masu rubutu daban-daban na nuna fushinsu kana abin da suka kira kisan gillar da ake yi wa mutane, da kuma "kunnen uwar shegu da hukumomi suka yi a kan lamarin".

Kafin wannan zanga-zanga ta Najeriya, wasu 'yan kasar mazauna Ingila sun yi irinta a Landan ranar Juma'a.

Sai dai a daidai lokacin da ake wannan maci, wanda har aka dangana da fadar shugaban kasar a Abuja, Shugaba Buharin yana birnin Amman na kasar Jordan inda yake halartar taron tattalin arziki na duniya.

Baya ga dumbin mutanen da suka fita tituna, wasu da dama kuma sun yi ta rubuta nasu sakonnin ne a shafukan sada zumunta da muhawara.

A shafin twitter an yi ta amfani da maudu'ai har kala uku da suka hada da #MarchForZamfara #SaveZamfara #ZamfaraIsBleeding.

Akasarin masu zanga-zangar sun sanya tufafi mai launin ja, don nuna yadda ake zubar da jinin al'ummar jihar ba tare da daukar matakin kawo karshen masifar ba.

Me masu zanga-zangar ke nema?

Hakkin mallakar hoto @abdulrazaq754
Image caption Wasu daga cikin masu zanga-zangar na kira ga Buhari da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara

Masu zanga-zangar dai na so a dauki matakan gaggawa ne don kawo karshen zubar da jini a Zamfara.

Suna kuma so a ayyana dokar ta-baci a jihar da gaggawa, tare da kai karin sojoji da 'yan sanda.

Sannan kuma suna so gwamnati ta nuna kulawa ga 'yan gudun hijirar da rikicin ya raba da muhallansu.

Suna kuma kira ga Shugaba Buhari da ya nuna kulawarsa da tausayawa kan halin da Zamfara ke ciki.

@AminuFaragai yana cewa: "ku gaya masa (Buhari) ya dawo gida da sauri domin duniya na ganin yadda ya banzatar da jama'arsa."

@el_shuaybb yana cewa ne a dakatar da kashe-kashe a Zamfara domin 'yan Zamfara su ma mutane ne.

@ozubulu_boy ya ce ai 'yan bokon Arewa ba su shirya ba ne, duk sanda suka shirya za su dauki mataki kan shugaba Buhari.

Me ke faruwa a Zamfara?

An shafe tsawon lokaci al'ummar jihar Zamfara na cikin halin ni-'yasu kan tabarbarewar tsaro.

'Yan fashi da masu garkuwa da mutane sun dade suna cin karensu babu babbaka, ta hanyar kai hare-hare kauyuka, suna kona gidaje da kashe mutane da kuma sace su.

Al'amarin ya sa har mutanen yankunan karkara suke kaura zuwa manyan garuruwa da birane na jihar da kuma makwabtan jihohi.

Wannan abu ya tagayyara dubban mutane ta hanyar raba su da muhallansu da asarar rayuka da dukiyoyi.

Me hukumomi ke yi?

Hukumomi dai sun sha yin ikirarrin cewa suna kokarin magance matsalar.

Sai dai 'yan kasar da dama na ci gaba da ganin gazawar gwamnatin tarayya da ta jiha.

A kwanan baya gwamnan jihar Abdul'aaziz Yari ya fito yana cewa ya cire kansa daga babban jami'in tsaro na jihar, saboda a cewarsa "ba ya iya tsawatar wa jam'ian tsrao na 'yan sanda ko sojojin da ke aikin wanzar da tsaro a jihar.

Duk da cewa Buhari na ikirarin ya samu nasarar murkushe mayakan Boko Haram tun bayan hawansa mulki a 2015, amma wasu na ganin rikicin Zamfara babban kalubale ne ga gwamnatinsa musamman a bangaren tsaro.

A lokacin da ya je yakin neman zaben 2019 a jihar, ya sha suka kan wani kalami da ya yi cikin raha, inda y ace: "Ya fi son a ci a koshi, idan ma fitinar za a yi sai a yi."

Wannan magana ta harzuka mutane tare da jawo ce-ce-ku-ce, inda da yawa ke ganin hakan rashin nuna damuwa ne kan kashe mutane da ake ci gaba da yi kusan kullum a jihar.

Ina Shugaba Buhari?

Hakkin mallakar hoto Presidency Nigeria
Image caption A wannan taron na kasar Jordan Shugaba Buhari dan gayya ne kawai

A ranar Alhamis ne Shugaba Buhari ya tafi yankin Gabas Ta Tsakiya domin halartar wani taron tattalin arziki a babban birnin kasar Jordan Amman.

Taron dai na tattalin arziki ne na duniya baki daya, wanda kuma zai mayar da hankali kan kasashen gabas ta tsakiya da kuma kasashen arewacin Afirka.

A wannan taro Shugaba Buhari dan gayya ne kawai, sai dai a ranar Asabar da al'ummar kasar suka dau dumi kan kasha-kashen Zamfara, a daidai lokacin ne shi kuma ya gabatar da kasida a wajen taron.

Kuma a ranar Lahadi zai tsallaka kasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato birnin Dubai, inda cen ma aka gayyace shi wani taron.

Da yawan mutane sun yi ta zargin Buhari bai damu da yawan kashe-kashen da ake yi a Zamfara ba, musamman yadda ya fito ya yi jaje kan kashe wani mutum da aka yi a Legas, amma bai jajantawa al'ummar Zamfara kan kashe musu mutum 40 da aka yi a ranar ba.

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Sharhi daga Kadariya Ahmed:

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun yi ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar.

A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala'i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar 'yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.

Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan 'yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan kato da gora suka fara kokarin ganin sun kare kansu da duk abin da ya kamata.

Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.

A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansu ba.

Abin da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

Daruruwan mutane sun mutu a 2018, kuma gwamman mutane sun mutu a 'yan watannin da suka gabata sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar Zamfara.

Sai dai saboda rashin isassun masu kawo bayanai, zai yi wahala a fadi adadin mutanen da suka mutu a rikicin da aka shafe shekara shida ana yi.

Labarai masu alaka