Mutum 21 sun mutu a rikicin Libya

Gen Haftar has ordered his forces to advance on Tripoli

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Janar Haftar ya umarci dakarunsa sun kwato Trabulus

Akalla mutum 21 ne suka rasa rayukansu, wasu gommai kuma suka sami raunuka a kwanaki hudu da suka gabata saboda rikicin da ya dabaibaye wasu sassa na Trabulus.

Masu fada da juna sun yi biris da kiraye-kirayen da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na a tsagaita bude wuta.

Wannan fadan dai ya fi kamari ne a yankunan kudancin birnin, inda wani janar na soja ke kokarin kwace birnin daga hannun gwamnatin kasar.

Barkewar sabon rikici na son yin kafar angulu da matakan diflomasiyya domin kawo sulhu a siyasance.

Wannan fadan na baya bayan nan tsakanin wadanda da ke iko da sassan kasar biyu ne, kuma ya shammaci masu shiga tsakani na kasa-da-kasa.

A cikin wani sako na Twitter, sakataren harkokin waje na Birtaniya, Jeremy Hunt ya ce kasarsa da Tarayyar Turai za su duba hanyoyin kashe wutar rikicin domin kawo karshen zubar da jini a Libya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wata kasuwa a birnin Trabulus. Mazauna birnin sun fara tara kayan amasarufi

Fada dai ya barke ne tsakanin dakarun da ke biyayya ga Janar Khalifa Hafter, wanda ke iko da yankin gabashin Libya, kuma yake adawa da gwamnatin Libyan da ke da shalkwatarta a birnin Trabulus.

A daya bangaren kuma akwai wasu kungiyoyi masu dauke da makamai da ke marawa gwamnatin kasar da ke iko da yammacin kasar.

Hukumar bayar da agaji ta MDD ta nemi bangarorin biyu su tsagaita fadan da suke yi na sa'a biyu domin a sami shigar da abinci da magunguna zuwa ga wadanda rikicin ya rutsa da su, amma abin ya ci tura.

Amurka ta janye wata rundunar sojojinta da ke cikin kasar - matakin da ake ganin na nuni cewa rikicin na iya kazancewa.