'Yan Sudan na neman sojoji su hambare Omar al-Bashir

President Bashir spoke to the National Dialogue Committee at his palace on 5 April

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba al-Bashir ya gana da wani kwamitin sulhu na Sudan a fadarsa ranar 5 ga watan Afrilu

A Sudan dubban masu zanga-zanga ne suka sake taruwa a dare na biyu suna neman Shugaba Omar al-Bashir ya sauka daga mukaminsa.

Da alama suna son sojojin kasar su hambare shugaban ne, kuma a kafa wata gwamnatin rikon kwarya kafin a yi zabe.

Wannan ne bore mafi muni ga mulkin al-Bashir da 'yan kasar suka yi tun watan Disambar bara.

Shugaba al-Bashir ya ki sauka daga mukaminsa, inda yake cewa masu adawa da shi su nemi mulki ta hanyar kayar da shi a zabe.

Kawo yanzu dai sojojin kasar ba su dauki wani mataki ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro sun rika amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga

A Khartoum, jami'an tsaro sun rika amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa dubban masu zanga-zangar da suka mamaye shakwatar sojojin kasa ta kasar.

Wannan zanag-zangar ta zo daidai da cika shekara 34 da juyin mulkin da al-Bashir yayi wa Shugaba Jaafar Nimieri.

Kawo yanzu dai rahoanni na cewa mutum daya ya rasa ransa a birnin Omdurman da ke tsallaken kogn Nil daga Khartoum.

Abin lura da shi a nan shi ne al-Bashir na neman 'yan adawa su bi hanyar demokradiyya, bayan shi da kansa juyin mulki yayi wa gwamnatin da yake adawa da ita.