An kama wanda kafa kamfanin kwarmata bayanai na Wikileaks, Julian Assange, a Landan

An kama wanda kafa kamfanin kwarmata bayanai na Wikileaks, Julian Assange, a Landan

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyon.

Shugaban kamfanin kwarmata bayanai na Wikileaks zai iya fuskantar wasu sabbin tuhume-tuhume kan zargin sa da ake yi na aikata fyade a Sweden.

An kama Assange mai shekaru 47 wanda aka baiwa mafaka a ofishin jakadancin kasar Ecuador da ke birnin Landan na tsawon shekaru bakwai.

Masu shigar da kara a kasar Sweden sun bayyana cewa suna gudanar da bincike kan lamarin bayan da lawyan wanda ake tuhuma ya bukaci hakan.

Amurka kuma tana so ta tasa keyar sa zuwa Birtaniya bayan da aka zarge shi da hannu a bayyana wani sirrin gwamnati mafi girma wanda aka taba bayyanawa a 2010.

Lawya Elizabeth Massi Fritz ta ce za ta yi duk abin da ya kamata domin ta ga an sake bude binciken a kasar Sweden.

Assange ya nemi mafaka a ofishin jakadancin da ke unguwar Knightsbridge a 2012 domin ya kaucewa tasa keyar sa zuwa gida kan tuhume-tuhumen da ake masa na aikata fyade.

Amma Ecuador ta janye kariyar da ta bashi kuma ta gayyaci 'yan sanda da su kama shi a ranar Alhamis.

Bayan da aka kama shi bayan an sha takaddama, an kai shi kotun Majistri ta Westminster, kuma a nan ne aka same shi da laifin sabawa sharuddan beli a Birtaniya.

Ya kwana a hannun 'yan sanda a daren Alhamis kuma yana fuskantar zama a gidan yari na shekara daya don wanan tuhumar.

Majalisar dinkin duniya ta yi kira da a girmama damar da yake da ita a yayin shari'ar da za a yi masa bayan an tasa keyarsa.