Ana ci gaba da alhinin rasuwar Justice Mamman Nasir

@JaafarSJaafar Hakkin mallakar hoto @JaafarSJaafar

Tun bayar rasuwar Galadiman Katsina Justice Mamman Nasir a ranar Asabar, jama'a da dama daga fadin Najeriya ke ci gaba da tururuwa zuwa gidan mamacin da ke karamar hukumar Malumfashi domin yi wa iyalensa ta'aziyya.

Haka ma, a shafukan sada zumunta na Intanet, jama'a da dama na ci gaba da ta'aziyya da nuna alhini bisa ga rashin mamacin, inda da dama ke bayyana cewa an yi babban rashi a kasar.

Kafin rasuwarsa, ya kasance daya daga cikin 'Yan Majalisar Sarkin Katsina inda ya ke da sarautar Galadiman Katsina hakimin Malumfashi.

Sa'annan kuma ya taba zama Ministan Shari'a na Arewacin Najeriya a 1961 inda ya shafe shekaru biyar kan mukamin.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi ta'aziyar rasuwar mamacin a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa wannan babban rashi ne ga kasa baki daya.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana marigayi Mamman Nasir a matsayin Alkali mara tsoro kuma mai aiki tukuru da ke tunkarar duk wani aiki da karfinsa da kuma kishi.

Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana mutuwar mamacin a matsayin mutuwar da baza a manta da ita ba inda ya ce marigayin ya taimaka kwarai wajen habaka bangaren shari'a da kuma kwato 'yancin bangaren domin kasancewar bangaren shari'a a matsayin mai cin gashin kanta.

Takaitaccen tarihin Justice Mamman Nasir

An haifi Justice Mamman Nasir a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya a shekarar 1929.

Ya yi karatun sakandare dinsa a Kwalejin Kaduna inda ya samu takardar shaidar kammala karanun sakandare ta WAEC a 1947.

Daga bisani ya tafi jami'ar Ibadan inda ya samu digiri a harshen Latin.

Daga nan kuma ya tafi makarantar horar da lauyoyi inda ya samu digiri a bangaren shari'a a 1956 kuma a wannan shekarar ce aka rantsar da shi a matsayin cikakken lauya a wata kotu da ke Ingila da ake yi wa lakabi da 'Licoln Inn.''

Ya dawo Najeriya a 1956 a matsayin lauya mai shigar da kara.

An nada shi Ministan Shari'a na Arewacin Najeriya a 1961 inda ya shafe shekaru biyar kan mukamin sai kuma daga baya ya zama darakta a ofishin lauyoyi masu shigar da kara na arewacin Najeriya a 1967.

A 1967 din dai Mamman Nasir ya zama babban lauya a ma'aikatar shari'a a jihar arewa ta tsakiya a wancan lokaci.

Ya rike wannan mukamin na shekaru bakwai inda daga nan ne aka nada shi alkalin kotun koli a 1975.

An kuma nada shi a matsayin shugaban kotun daukaka kara, mukamin da ya rike kenan har zuwa 1992 inda daga nan ne ya zama Galadiman Katsina.

An nada shi a matsayin Galadiman Katsina a ranar 9 ga watan Mayun 1992.

Ya kuma rasu ranar Asabar 13 ga watan Afrilun 2019.