Gobara ta tashi a Majami'ar Notre-Dame a Faransa

Notre-Dame Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekarar bara Cocin Katolika ta nemi tallafin kudi don gyara ginin mai shekara 850 a duniya

Gobara ta tashi a shahararren ginin Cocin Notre-Dame a birnin Paris na kasar Faransa, inda nan take ta mamaye ginin.

Zuwa yanzu dai ba a san musabbabin gobarar ba da ta mamaye ginin majami'ar mai shekara 850.

Amma hukumomi sun ce ba zai rasa nasaba da aikin kwaskwarima da ake yi wa ginin ba.

Ana ci gaba da ayyukan shawo kan wutar, inda rufin majami'ar da kuma hasumiyarta suka kone kurmus.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane kenan ke kallon ginin na ci da wuta a gabar kogin Seine da ke tsakiyar birnin Paris

A shekarar bara Cocin Katolika ta nemi tallafin kudi don gyara ginin, wanda ya fara tsattsagewa.

Wani mai magana da yawun hukumar kashe gobara a Paris ya ce nan da sa'a daya da rabi mai zuwa za a iya tabbatar da ko za a iya kawo karshen wutar ko kuma a'a.

Shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron da tuni ya je wajen ya ce hankalinsa na kan "'yan darikar Katolika da kuma al'ummar Faransa."

"Kamar sauran 'yan kasa, ban ji dadin ganin wani bangare namu yana konewa ba."

Labarai masu alaka