Da gaske kasar Canada na bukatar 'yan ci-rani daga Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Labarin da ke cewa kasar Canada na bukatar 'yan ci-rani har miliyan daya daga Najeriya ba gaskiya ba ne, kamar yadda ofishin jakadancin kasar a Najeriya ya bayyana.
A farkon makon nan ne aka wayi gari da wani labarin da ke cewa Firai Ministan kasar Canada Justine Trudeau ya roki Shugaba Buhari da ya bai wa kasarsa 'yan ci-rani milyan daya daga Najeriya.
An yada wannan labari a shafukan Intanet da dama da kuma na sada zumunta.
Asalin hoton, The News Chronicle
Shafin The News Chronicle ya wallafa labarin a ranar 16 ga watan Afrilu
Shafin The News Chronicle ya wallafa labarin da kanun cewa: "Firai Ministan Canada ya roki 'yan ci-rani miliyan daya daga Najeriya".
Alakar 'yan Najeriya da kasar Canada mai karfi ce, inda wasu 'yan kasar suka dade suna sha'awar zuwa kasar.
Jim kadan bayan hukumar zabe ta INEC ta sanar da dage babban zaben 2019, kafin daga bisani a gudanar da shi, 'yan kasar suka fara tafka muhawara kan kowace kasa ya kamata su koma da zama.
Sun yi hakan ne don yin ba'a ga mahukunta saboda gazawarsu wajen gudanar da zaben. Nan take kuma suka yanke shawarar koma wa Canada.
Abin da Canada ta ce
Ofishin jakadancin Canada a Najeriya ya musanta wannan labari a wani jerin sakonni a shafinsa na Twitter.
"Idan ka ci karo da wannan labari a shafinka na sada zumunta, to ka sani ba gaskiya ba ne. Domin samun bayanai kan balaguro zuwa Canada ka ziyarci wannan shafin,"in ji wani sakon Twitter daga ofishin.
Ofishin ya kara da cewa a shekarar 2017 kadai an bai wa 'yan Najeriya 4,200 shaidar zama a kasar ta din-din-din, wanda ya ninka yawan wadanda aka bai wa a shekarar 2016.
"'Yan Najeriya mazauna Canada suna bai wa kasashen biyu kyakkyawar gudunmuwa," in ji ofishin.
Mene ne labarin karya?
Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.
Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.
Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.
A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.
Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al'umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe.
Binciken da BBC ta yi a kwanakin baya ya gano cewa labaran karya na sahun gaba wurin yada rikicin da ake fama da shi a Najeriya tsakanin makiyaya da manoma.
Hakan ne kuma ya sa ma'aikatar sadarwa ta kasar kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi'a, wacce ke kara samun gindin zama a kasar, musamman a shafukan sada zumunta.
Yadda ake gane labaran karya
Akwai yiwuwar ci gaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokutan zabuka.
Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:
Asalin hoton, AFP
Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.
Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.
Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.
Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?
Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa.
Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.
Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita.
Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.
Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.