Europa: Chelsea da Arsenal sun je daf da karshe

Chelsea Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Chelsea da ta Arsenal sun kai zagayen daf da karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa ranar Alhamis.

Chelsea ta yi nasarar doke Slavia Praque 4-3 a Stamford Bridge, jumulla kwallo 5-3, bayan da Chelsea ta ci 1-0 a wasan farko a makon jiya.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta ci kwallaye ta hannun Pedro Rodriguez wanda ya ci biyu da wadda Simon Deli ya ci gidansu sai wadda Olivier Giroud ya zura a raga.

Ita kuwa Slavia ta ci nata kwallayen ne ta hannun Tomas Soucek da kuma Petr Sevcik wanda shima ya ci biyu a karawar..

Arsenal kuwa ta yi nasarar cin Napoli 1-0, bayan da a wasan farko Gunners ta ci 2-0 a Emirates, jumulla 3-0.

Da wannan sakamakon kungiyoyin Ingila biyu sun kai zagayen daf da karshe, kamar yadda Tottenham da Liverpool suka yi irin wannan bajintar a Champions League.

Valencia ma ta kai zagayen daf da karshe bayan da ta doke Villareal 5-1 gida da waje.