'Shugabannin kananan hukumomi ne ke rusa ganuwar Kano'

Aliko Dangote da Sarkin Kano

Asalin hoton, FadarKanotaDabo

Bayanan hoto,

Aliko Dangote da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, ya koka kan irin koma baya da ake samu ta bangaren tattalin arziki a Kano da kuma bangaren raya al'adu.

Ya bayyana haka ne a wajen wani taro a jahar Kano da ke arewacin Najeriya kan bunkasa tattalin arzikin jahar karkashin jagorancin wata kungiyar matasa da dattawa.

A wajen taron wanda aka gudanar da shi a sashen koyar da cinikayya na Dangote dake jami'ar Bayero ta Kano, an tabo dalilan da suka kawo durkushewar masana'antu da kuma kauracewa Kano da masu zuba jari suke yi.

A yayin taron wanda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II da Alhaji Aliko Dangote suka jagoranta, an mayar da hankali kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin Kano.

An tattauna kan yadda za a samar da wasu hanyoyin farfado da kamfanonin da ake da su a jahar.

Aliko Dangote ya koka kan yadda ake rufe kamfanoni a birnin inda ya ce "babu dalilin da kamfanoni za su rika kasancewa a Kano, domin shi kamfani dalilinsa na gazawa bai wuce rashin wutar lantarki ko rashin kasuwa ba."

Ya kuma bayyana cewa "a Kano, abin da muke samu na yawan wutar lantarki bai wuce megawatt 40."

Daidaitar da wuraren tarihi

Rashin kula da wuraren tarihi na daga cikin dalilai da aka bayyana da cewar sune kashin bayan kara durkushewar samun kudin shiga da kuma tattalin arzikin jihar ta Kano.

Ana rushewa tare da yin gine-gine a kan ganuwar da ta kewaye kwaryar birnin Kano duk da irin kudaden da kasashen ketare ke bayarwa don a sake gina ta.

Ga abin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce:

"Wannan ganuwar ta Kano, yanzu an rarraba ta. An yi shaguna, an yi gidaje."

Sarkin ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ake rushe tarihi da gadon kasar Kano:

"Ganuwar da ita ce tarihinmu na Kano, sai wani chairman (shugaban karamar hukuma) da bai san darajar tarihinsa ba, ina zai shugabanci al'umma?"

Ya kuma ce "tarihinmu na shekara 700 ya zama shago".

Sarkin dai ya umarci Aliko Dangote da Abdulsamad Isiyaka Rabiu da su sake gina ganuwar Kano tun da suna da kamfanin siminiti, inji sarkin.

Asalin hoton, FadarKanotaDabo

Sai dai gwamnatin jihar ta Kano ta ce ko kadan ba laifinta ba ne yadda wasu ke gine-gine akan ganuwar.

Ta dora alhakin hakan kan kananan hukumomin jihar da ganuwar ta fada a ciki.

Kuma ta tabbatar da cewar gwamnati za ta dauki matakin da ya dace kan wannan matsala.

Ahmad Rabi'u shi ne kwamishinan ciniki da masana'antu da yawan buda idanu na jihar Kano.

"Daga karamar hukuma maganar ta ke.

"Amma a matakin gwamnati, akwai wani shiri na fadada bukukuwan sallah, domin gwamnati ta san cewa abubuwan tarihi na cikin abubuwa ma su bunkasa tattalin arzikin kasa."

Asalin hoton, KASSIM TURAKI

Bayanan hoto,

Fadar Sarkin Kano

Masana tarihi kamar Dr. Tijjani Muhammd Naniya, wanda malami ne a tsangayar tarihi da ke jami'ar Bayero ta Kano sun bayyana kalaman sarkin na Kano a matsayin wata matashiya ce da za ta karawa kiran da aka jima ana yi wa gwamnatin jihar da ta kawo karshen yadda ake rushe ganuwar, tare da tayar da gine-gine musamman na shaguna akanta.

Ana dai yi wa Kano kallon cibiyar kasuwanci a Najeriya da ma wasu yankunan kasashen Afirka ta yamma har zuwa Sudan.

Amma bincike ya nuna cewar akwai kimanin matasa marasa aikin yi fiye da miliyan 3, kuma ba ta amfani da su yadda ya kamata.