Shehu Sani: Masu yawon shakatawa su kaurace wa Kaduna saboda tsaro

sanata Shehu Sani

Gwamnatin jihar Kaduna ta Najeriya bayyana rashin amincewarta da shawarar Sanata Shehu Sani ya bayar cewa, ya kamata 'yan yawon shakatawa su nisanci zuwa jihar a halin yanzu.

Sanata Shehu Sani na wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ne.

Sanatan ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari wajen wani wurin yawon shakatawa da ke Kajuru.

"Yawon shakatawa kan yiwu ne idan akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya. A halin yanzu a cikin jihar Kaduna, har da wasu jihohi da ke makwabtaka da Kaduna kamar Zamfara da Katsina, ba ka cewa akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali," inj sanatan.

Ya kara da cewa "A halin gaskiya, babbar shawara da za a iya ba jama'a masu yawan shakatawa, ita ce su dakata domin wannan ba lokaci ne na shakatawa ba.

Ya ce wannan lokaci ne na addu'a kuma lokaci ne da shugabannin da jama'a suka zaba, da wakilan da suka zaba su tashi tsaye domin kare su, su kuma kare kasar nan daga halin rashin tsaro da ake ciki.

Siyasa Shehu Sani ke yi - Gwamantin Kaduna

Amma gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani ga sanatan, inda ta ce ba ta amince da matsayar da ya dauka kan batun ba, musamman kiran da yayi na baki masu yawon shakatawa su kauracewa jihar saboda matsalar tsaro.

Kakakin gwamnatin jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ya mayar wa sanata Shehu Sani martani:

"Duk wani mai kishin kasar nan, ba zai fito yana gargadin mutane kar su ziyarci jiharsa ba."

Mista Aruwan ya ce Sanatan ya furta wadannan kalaman ne domin wasu dalilai na siyasa.

Ya kara da cewa "Babu wata jiha ko wata kasa da ba ta da matsalolin tsaro. Ko a karshen makon nan an aki wa kasar Sri Lanka hare-haren ta'addanci."

A sanadiyyar harin da aka kai a garin Kajuru na jihar Kaduna, maharan sun halaka wata baturiyar Birtaniya mai suna Faye Mooney da wani dan Najeriya mai suna Matthew Oguche.

Dukkan wadanda aka kashen ma'aikatan agaji ne masu aiki a Najeriya.

Sun kuma yi awon gaba da wasu mutum uku, wanda a halin da ake ciki suna garkuwa da shu a wani wurin da kawo yanzu ba a sani ba.