Sojoji sun dakile wani hari a Benue

Makamai da sojoji suka kwato

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto,

Rundunar sojan Najeriya tana gudanar da aikin samar da zaman lafiya na musamman a jihar Benue

Dakaru na musamman na runduna ta 72 masu aikin kiyaye zaman lafiya a jihar Benue sun dakile wani rikicin kabilanci a jihar da safiyar Litinin.

Kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter, rundunar sojojin Najeriya ta ce wasu 'yan fashi ne ke yunkurin kai hari kan al'ummar karamar hukumar Katsina-Ala, inda cikin hanzari ta dakile yunkurin na su.

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar saka dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 a karamar hukumar ta Katsina-Ala.

Hakan ya biyo bayan wani rikicin kabilanci tsakanin kabilun Shitile da Ikyora.

Rahotanni na cewa rikicin ya yi sanadin rasa ran mutum 11 da kuma batan wasu da dama.

Rundunar ta ce: "Dakaru na musamman na runduna ta 72 masu aikin kiyaye zaman lafiya a karamar hukumar ta Katsina-Ala ta jihar Benue sun dakile wani rikicin kabilanci tsakanin Tiv clans-Shitile da Ikyora ranar Litinin 22 ga Afrilu.

"Wannan ya biyo bayan wasu bayanan sirri ne game da harin da wasu 'yan fashin Shitile suka shirya kaiwa kan garin Katsina-Ala," in ji rundunar.

Rundunar kuma ta samu nasarar kwato makamai da suka hada da manyan bindigogi.

Jihar Benue ta sha fama da rikicin kabilanci tsakanin manyan kabilu a jihar, wanda ya yi sanadiyyar kisar mutane da dama.

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya a jihar da ma sassan kasar da dama.

A watan Afrilun bara Majalisar Wakilai ta gayyaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya bayyana a gabanta domin yin bayani game da rikicin jihar.

Rikicin manoma da makiyaya

Asalin hoton, AFP

Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu, al'amarin da ya jawo hankalin kusan daukacin 'yan Najeriya.

Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.

A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan kira, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar domin kiwo.

Amma a watan Fabrairu, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.