Dalibar da ta zama jigo wajen hambarar da al-Bashir

Dalibar da ta zama jigo wajen hambarar da al-Bashir

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

Alaa Salah wata daliba 'yar shekara 22 ta zama tauraruwa mai fafutika a juyin juya halin Sudan.

Ita ce ta jagoranci zanga-zangar hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir.

Bidiyonta ya yadu sosai kuma mutane sun dauke ta a matsayin wata sabuwar alama a kasar saboda irin karfin gwiwar da ta nuna tare da sauran mata.

''Mu ba mu ji tsoro ba, amma mun san komai zai iya faruwa. A lokacin za a iya harbe mu ko kuma a yi mana illa.'' inji ta.