Shin da gaske an haifi jariri da rubutun dawowar Annabi Isa a hannunsa?

Hoton jariri Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama sun yada hoton ne da nufin cewa bai wa ce ga Najeriya

Daruruwan mutane ne a Facebook suka yada wani hoto da ke dauke da wani jariri, wanda aka ce an haife shi tare da wani sako game da dawowar Annabi Isa a hannunsa.

An yi ikirarin cewa an haifi jairin ne a wajen Abuja babban birnin Najeriya, amma kamfanini dillancin labarai na AFP ya gano cewa an dauki hoton ne a garin Maiduguri a jihar Borno.

An yada labarin sau kusan 242,000 tun daga 21 ga watan Satumbar 2017.

Mafi yawan wadanda suka yada wannan hoton dai yawancinsu mabiya addinin Kiristoci ne saboda sun dauki abin a matsayin bai wa ce ga Najeriya.

Bincike ya nuna cewa hoton ya bulla kafar Intanet watanni kafin a fara wannan ikirarin, kuma shafin Unimaid Gossip ne ya fara wallafa shi a shafin Twitter a ranar 26 ga watan Mayun 2017.

Shafin ya yi wa hoton taken: "An tsinci wani jariri maras rai a dakin kwanan dalibai mata na Jami'ar Maiduguri".

Hakkin mallakar hoto AFP

Kuma da aka bincika jerin kalmomin "Unimaid female hostels" a Google an gano cewa wasu daga cikin jaridun Najeriya sun ruwaito wannan labarin.

Rahoton da jaridar The Cable ta yi, ya nuna wani hoto na daban na matar a ranar 25 ga watan Mayu.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu tsofaffin daliban jami'ar guda uku Enyigwe Peter da Baraya Bala Abdullahi da kuma Naomi Joda Dibal duk sun tabbatar da faruwar hakan.

Naomi Joda Dibal wadda take yin digirinta na biyu yanzu haka a jami'ar, ta bayyana cewa abin ya faru ne a dakin kwana na Murtala.

"Abin da ya faru ranar shi ne, wata daliba ce da ba a gano ko wace ce ba ta yar da jaririn. Bayan an gan shi ne wannan matar wadda ita ce mai kula da dakin ta isa wajen kuma ta dauko shi," kamar yadda ta shaida wa kamfanin AFP.

Menene labarin karya?

Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.

Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.

Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.

A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.

Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al'umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe.

Binciken da BBC ta yi a kwanakin baya ya gano cewa labaran karya na sahun gaba wurin yada rikicin da ake fama da shi a Najeriya tsakanin makiyaya da manoma.

Hakan ne kuma ya sa ma'aikatar sadarwa ta kasar kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi'a, wacce ke kara samun gindin zama a kasar, musamman a shafukan sada zumunta.

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar ci gaba da samun labaran karya, musamman a lokutan zabuka.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.

Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.

Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa.

Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita.

Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani.

Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.